Kungiyar Matasan Kauru (KYA) ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, da ya cika alkawuran da ya yi na gina titunan cikin garin Kauru da kuma inganta samar da wutar lantarki a Karamar Hukumar ta Kauru.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta yaba wa gwamnan bisa ginawa tare da kaddamar da titin Pambeguwa–Kahuta–Kauru mai tsawon kilomita 21, inda ta bayyana aikin a matsayin babban ci gaba da ya inganta harkokin tattalin arziki da rayuwar al’ummar yankin.
Matasan sun ce titin ya dade yana jefa mazauna yankin cikin wahala, musamman a lokacin damina, lamarin da ke kawo cikas ga sufuri, noma da samun muhimman ayyukan jin kai.
Kungiyar ta tunatar da cewa, lokacin da Gwamna Uba Sani ya kaddamar da titin a ranar 4 ga watan Fabrairun 2026, ya yi alkawarin aiwatar da wasu ayyukan raya kasa, ciki har da gina titunan cikin garin Kauru da kuma magance matsalar rashin ingantacciyar wutar lantarki.
KYA ta bayyana cewa har yanzu garin Kauru, hedikwatar karamar hukumar, na fama da rashin ingantattun tituna, inda da dama daga cikinsu ba a iya bins a lokacin damina. Sun ce hakan na hana zirga-zirga cikin sauki tare da kawo cikas zuwa ga kasuwanni, makarantu, cibiyoyin lafiya da unguwanni.
Kungiyar ta kuma nuna damuwarta kan rashin tabbatacciyar wutar lantarki da yankin ke fama da ita tsawon shekaru da dama. A cewarta, hakan ya shafi harkokin kasuwanci, da rage zuba jari, tare da kawo cikas ga ilimi da ci gaban tattalin arziki.
Matasan sun yabawa gwamnatin jihar bisa amincewa da ayyukan gina titunan cikin gari a Zariya, suna mai cewa hakan alama ce ta kudurin gwamnatin na bunkasa ababen more rayuwa a fadin jihar Kaduna.
Sai dai kungiyar ta bukaci Gwamna Uba Sani da ya fadada irin wannan ci gaba zuwa Kauru domin cika alkawuran da ya yi wa al’ummar yankin lokacin da ya ziyarce su.
Kungiyar ta sake jaddada goyon bayanta ga gwamnatin jihar, tare da bayyana yakinin cewa gwamnan zai tabbatar da adalci wajen rabon ayyukan ci gaba a dukkan sassan jihar.
A karshe, ta yi kira ga gwamnan da ya amince da aikin gina titunan cikin garin Kauru tare da kara kaimi wajen inganta wutar lantarki a yankin, da kuma fatan za a cika alkawuran da aka yi wa al’ummar Kauru nan ba da jimawa ba.
Daga Yusuf Zubairu Kauru







