Gidauniyar Tagwaye Ta Ba Da Jini Kyauta A Asibitin Nuhu Bamalli

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Shugabar Sashen Adana Jini na Asibitin Nuhu Bamalli da ke Kano, Hajiya Fa’iza Aminu Isa, ta yaba wa Gidauniyar Taimakawa Tagwaye Maza da Mata ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, bisa gudunmawar jini da ta bayar ga marasa lafiya a asibitin.

Ta ce gudunmawar ta zo ne a lokacin da ake tsananin buƙatar jini, lamarin da zai taimaka wajen ceton rayukan marasa lafiya, musamman mata masu haihuwa da ke fuskantar matsalar rashin jini.

Hajiya Fa’iza ta bayyana cewa ba wannan ne karo na farko da gidauniyar ke kai irin wannan taimako ba, domin a shekarar da ta gabata ma ta ba da irin wannan gudummawa.

“A wasu lokuta mata kan zo haihuwa cikin gaggawa ba tare da samun jini ba, har sai danginsu sun fita neman masu bayar da jini. Wannan taimako zai rage irin wannan wahala, musamman ga iyalai marasa ƙarfi,” in ji ta.

Ta ƙara da cewa jinin da aka tara zai taimaka wa marasa lafiya a Asibitin Nuhu Bamalli, kuma idan buƙata ta taso, za a iya tura wani kaso zuwa Asibitin Yara na Hajiya Bayero.

Hajiya Fa’iza ta kuma yi kira ga sauran ƙungiyoyi da masu hannu da shuni su yi koyi da gidauniyar wajen gudanar da irin wannan aikin alheri.
A nasa jawabin, Shugaban Gidauniyar Taimakawa Tagwaye Maza da Mata ta Ƙasa, reshen Jihar Kano, Alhaji Alhusain Abdullahi, ya ce taken gidauniyar shi ne “Ƙaunar Juna da Taimakon Juna.”

Ya ce sun kai ziyarar ne domin ba da gudunmawar jini kyauta ga marasa lafiya, yana mai cewa wannan na daga cikin ayyukan jin ƙai da gidauniyar ke gudanarwa a duk lokacin taronta na shekara-shekara.

Ya bayyana cewa a wannan karon, tagwaye sama da 20, waɗanda adadinsu ya kai kusan mutum 50, ne suka bayar da kusan ledojin jini 50.
Alhaji Alhusain ya ce baya ga bayar da jini, gidauniyar na gudanar da wasu ayyukan tallafa wa al’umma da suka haɗa da ɗaukar nauyin magunguna, yi wa yara kaciya, ba da magungunan ido da kuma rabon tabarau ga masu matsalar gani.

Ya kuma yabawa mambobin gidauniyar bisa haɗin kai da goyon bayan da suke ba shugabancinta, yana mai cewa hakan ne ke ƙara wa gidauniyar ƙarfin ci gaba da gudanar da ayyukan jin ƙai.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum