Sardaunan NATA, Mataimakin Shugaban Kungiyar Masu Maganin Gargajiya na Jihohi Bakwai na Shiyyar Arewa Maso Yamma, Alhaji Mukhtar Lamir Jibrin, ya bayyana godiyarsa ga Sarkin Maganin Gargajiya na Kano, Dakta Rabilu Muhammad bisa yadda ya duba darajar gidansu ya nada dan uwansa, Alhaji Jamilu Lamir, a matsayin Sarkin Magani na Karamar Hukumar Fagge.
Alhaji Mukhtar ya ce shi da yan uwansa suna alfahari da Jamilu a kowane lokaci.n mahaifinsa yana alfahari da wannan yaro. Yakan ce ya haifi daya tamkar goma. “Muna farin ciki sosai da wannan nadi da aka yi masa.”
Ya kuma yi godiya ga Sarkin Maganin Kano, yan majalisarsa, fadawa da sauran sarakunan magani irinsu Sarkin Shinfida, Alhaji Sani Muhammad Tsamiya Babba, Waziri, Madaki, Galadima, da Magajiya bisa karamci da girmamawar da suka nuna wa iyalan marigayi Lamir Jibrin.
Sardaunan NATA ya bayyana cewa sabon Sarkin ya cancanci wannan sarauta ne saboda biyayyarsa ga iyaye da biyayya gare sune jigo na samun daukaka a kowane lamari. Wanda ya rike iyaye da kyau Allah zai daukaka shi.
Ya shawarci matasa da su yi biyayya ga iyaye a cikin abin da bai sabawa Allah ba, su yi hakuri, su zauna da lafiya dajin maganar manyansu.
Yace: Idan kuka rike Uba da Uwa da kyau, da yardar Allah akwai nasara a gobe. Hakan zai sa ku taka matsayin da ba ku zata ba.”_
Alhaji Mukhtar Lamir ya yi addu’ar Allah ya wa masu mulki jagora, ya ba su lafiya da karin arziki, kuma ya shiryar da duk mai yin daidai ya kara masa.






