Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Ƙaramar Hukumar Birnin Kano ta bayyana aniyarta ta tallafa wa Gidauniyar Taimakawa Tagwaye Maza da Mata, bisa irin ƙoƙarin da take yi wajen haɗa kan jama’a, ƙarfafa zumunci da tallafa wa al’umma a fannoni daban-daban.
Shugaban Majalisar Kansilolin Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Hon. Yahaya Abdullahi Sabo, wanda aka fi sani da “Mai Duniya”, ne ya bayyana hakan a lokacin da ya jagoranci kansilolin wajen wakiltar Shugaban Ƙaramar Hukumar, Hon. Salim Hashim, a wani taron gidauniyar da aka gudanar a Rufaffen Ɗakin Wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata.
Hon. Yahaya Mai Duniya, wanda shi ne Kansilan Mazaɓar Shahuchi, ya ce taron na da muhimmanci saboda yana haɗa tagwaye da iyalansu tare da samar da damar taimaka wa mabuƙata.
Ya ce, “Wannan taro taro ne mai albarka da muhimmanci. Shugaban Ƙaramar Hukumar da kansa ya so ya halarta, amma wani uzuri ya hana shi.”
Ya ƙara da cewa gidauniyar tana bayar da gagarumar gudunmawa ga al’umma ta hanyar taimaka wa jama’a, tallafa wa manufofin gwamnati da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin al’umma.

A cewarsa, a matsayinsu na wakilan jama’a daga mazaɓu 13 na Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, za su bai wa duk wani shiri da ya shafi tallafawa tagwaye kulawa ta musamman.
“Nan gaba, Ƙaramar Hukumar za ta bayar da gudunmawar da ta dace wajen tallafa wa wannan ƙungiya,” in ji shi.
Tagwaye Sama Da 3,000 Ne Suka Yi Rajista
A nasa jawabin, Shugaban Gidauniyar Tagwaye ta Jihar Kano, Injiniya Alhussain Abdullahi, ya bayyana cewa sama da set 3,000 na tagwaye ne suka yi rajista da gidauniyar, yayin da adadin waɗanda ba su yi rajista ba ya haura hakan.
Ya bayyana cewa daya daga cikin manyan ƙalubalen da gidauniyar ke fuskanta shi ne ƙarancin kuɗaɗen gudanar da ayyukan tallafawa tagwaye.
Ya ce a wasu lokuta idan suka kai ziyara ga wata uwa mai tagwaye da ke cikin mawuyacin hali, suka tabbatar da cewa tana buƙatar taimako, sukan buƙaci lokaci domin su tattara abin da za su iya bayarwa.
“Wasu sukan ɗauka cewa mu ’yan siyasa ne ko kuma ma’aikatan gwamnati. Amma ba haka ba ne. Mutane masu hannu da shuni kaɗan ne a cikinmu. Duk wani taimako da muke bayarwa, muna haɗawa ne daga cikinmu sannan mu kai wa waɗanda suke buƙata, kama daga abinci, kayan kula da lafiya da kuma jari,” in ji shi.
Ya buƙaci waɗanda suke buƙatar taimako da su riƙa ba gidauniyar lokaci domin tattara abubuwan da za ta iya taimakawa da su.
Gidauniyar Ta Buƙaci Gwamnati Ta Shiga Tsakani
Injiniya Alhussain ya yi kira ga gwamnati da ta shiga cikin ayyukan gidauniyar ta hanyar tallafa mata, yana mai cewa gwamnati ita ce uwar kowa kuma tana da alhakin kula da harkokin lafiya, ilimi da jin ƙai.
Ya ce gidauniyar ta ɗauki nauyin tallafawa tagwaye ne gwargwadon ƙarfinta, don haka akwai buƙatar gwamnati ta taimaka mata domin ƙara faɗaɗa ayyukanta.
A cewarsa, akwai tagwaye masu ilimi daban-daban da ke neman aikin yi, yayin da gidauniyar kuma take ƙoƙarin koyar da sana’o’i da bayar da jari ga waɗanda ke buƙata.
Ya roƙi gwamnati da ta yi amfani da yawan tagwayen da ke cikin jihar wajen samar musu da shirye-shiryen koyon sana’o’i da tallafin jari.
Ya kuma buƙaci a taimaka wa waɗanda iliminsu bai kai matakin da ake buƙata ba su koma maƙaranta domin ƙara karatu.
Tagwaye Daga Sassa Daban-Daban Sun Halarci Taron
Shi ma ɗaya daga cikin shugabannin gidauniyar, Alhussain Abdullahi, ya ce rana ta biyu na taron ta samu halartar tagwaye daga sassa daban-daban.
Ya bayyana taron a matsayin wani dandali na nuna kauna, soyayya, zumunci da taimakon juna.
“Taro ne na nuna ƙauna, soyayya, zumunci da taimako. Mun raba tufafi, abinci da jari, inda iyaye da yara da marayu da dama suka amfana,” in ji shi.
Ya bayyana fatan cewa Majalisar Ƙaramar Hukumar Birnin Kano da wakilanta da suka halarci taron za su taimaka wajen samar wa gidauniyar tallafi, da koyar da tagwaye sana’o’i, tare da taimaka musu wajen samun ayyukan yi a ɓangarorin da suka ƙware.








