Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Al’umma daga sassa daban-daban na cikin gida da wajen Jihar Kano ne suka halarci bikin naɗin Alhaji Abdullahi Abubakar BK-BK a matsayin sabon Sarkin Matasan Masu Maganin Gargajiya na Jihar Kano.
An gudanar da bikin nadin ne a Fadar Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano.
Sarkin Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Alhaji Dakta Rabilu Muhammad, ya bayyana cewa an yi wa Alhaji Abdullahi Abubakar BK-BK nadin ne bisa cancanta da kuma irin gudunmawar da yake bayarwa wajen inganta lafiyar al’umma da kuma samar da ayyukan yi ga matasa.
Sarkin Maganin Gargajiyar ya hori sabon Sarkin Matasan da ya riƙe gaskiya da amana, tare da ci gaba da yin biyayya ga Majalisar Masarautar Maganin Gargajiya ta Jihar Kano domin kiyaye martaba da mutuncin masarautar.
A nasa jawabin, sabon Sarkin Matasan Masu Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Alhaji Dakta Abdullahi Abubakar BK-BK, ya bayyana farin ciki da jin daɗinsa bisa wannan karamci da ƙauna da Masarautar ta nuna masa.
Ya yi alƙawarin ci gaba da bai wa Masarautar haɗin kai da biyayya, da kare martabarta, da kuma bayar da gudunmawa wajen inganta lafiyar al’umma ta hanyar amfani da ilimin maganin gargajiya da suka gada daga iyaye da kakanninsu.
BK-BK ya kuma miƙa godiyarsa ga dukkan jama’a, ’yan’uwa, abokan arziƙi, masu sana’ar maganin gargajiya da mambobin Majalisar Masarautar bisa taya shi murnar wannan naɗin.
Daga cikin manyan baƙin da suka halarci bikin akwai Sarkin Shimfiɗa na Masu Maganin Gargajiya na Jihar Kano, Alhaji Sani Muhammad Tsamiya Babba, wanda ya bayyana jin daɗinsa bisa naɗin da aka yi wa BK-BK, da kuma naɗin Hajiya A’isha Rabilu a matsayin Fulani ta gidan Sarkin Magani.
Ya yi addu’ar Allah Ya sanya alheri a cikin waɗannan naɗe-naɗe, tare da fatan sabbin masu riƙe da sarautun za su yi amfani da matsayinsu wajen haɗa kan masu maganin gargajiya da kuma bayar da gudunmawa ga ci gaban al’umma.







