Wata matar aure mai suna Hadiza Abdullahi, ta nemi Kotun Shari’a da ke Magajin Gari a Kaduna, ta raba aurenta da mijinta, Isa Usman, bisa zargin rashin nuna mata soyayya da ƙauna.
Kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito, Hadiza, ta hannun lauyanta, Abubakar Suleiman, ta shaida wa kotun cewa ba ta ƙaunar mijinta, kuma ba za ta iya ci gaba da zaman aure da shi ba.
Saboda haka, ta roƙi kotun da ta raba aurensu ta hanyar khul’i, wato hanyar da mace ke neman a raba aurenta ta hanyar mayar da sadakin da aka ba ta.
Lauyan matar ya shaida wa kotun cewa an shafe shekaru 35 da aurar da Hadiza, inda aka biya Naira 1,000 a matsayin sadaki.
Ya ce matar ta shirya mayar da wannan kuɗi ga mijinta domin mijin nata ya sawwaƙe mata.
Sai dai lauyan mijin, I.T. Sanusi, ya ce wanda yake karewa bai iya tuna ainihin adadin sadakin da ya biya ba, amma ya tabbatar da cewa ya fi Naira 1,000.
Ya kuma bayyana cewa mijin na neman a biya shi Naira dubu 300, inda ya roƙi kotun ta ba su lokaci domin gabatar da shaidar adadin sadakin da aka biya da kuma dalilin buƙatar wannan kuɗi.
Alƙalin kotun, Yakubu Abdullahi, ya ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 2 ga Satumba, domin bai wa matar damar gabatar da hujjojin da za su taimaka wa kotun wajen yanke hukunci.








