By Ibrahim Muhammad Kano.
Fitacciyar jagora a kasar Hausa kuma mai fafutukar tabbatar da zaman lafiya, Ambassador Hajiya Samira Bala Usman “Tauraruwar Kasar Hausa, Jagaban Matan Najeriya”, ta yi kira ga mata da matasa da su yi amfani da yancinsu na ‘yan kasa don ganin an gudanar da yakin neman zabe da zaben 2027 cikin zaman lafiya.
Hajiya Samira ta bayyana mata da matasa a matsayin “ginshikin nasarar kowane zabe. Ta ce lokaci ya yi da za su yi amfani da wannan damar wajen zabar wanda ya cancanta, ba wanda zai yi amfani da su wajen biyan bukatun kansa na son rai da cutar da al’umma ba.
Ta ce “Matasa maza da mata ku fito ku zabi abin da zai bunkasa cigaban kasar nan. Kada ku yarda a ba ku dan abin da bai taka kara ya karya ba. Domin zai cutar da karamar hukumar ka, jiharka da kasarka, ya kuma jefa ku cikin wahala na tsawon shekaru hudu.”
“Tauraruwar” ta kuma yi kira ga mata da su fito da karfin gwiwa su zabi shugabanni masu adalci, masu kishin cigaban kasa da mutanen kirki.
Haka zalika ta gargadi matasa da kada su bari a ba su kudi ko kayan maye domin a tura su tayar da hankalin al’umma.
Ta ce: Wadanda za su sa ku aikata ba daidai ba da zarar sun ci zabe ba za su kara ganin ku ba. Ba za su taimake ku da ilimi, ko aiki, ko wani abu na kyautata cigabanku ba. Ana amfani da ku ne kawai lokacin yakin neman zabe.”
Ta kara da jaddada cewa matasa su nuna kyakkyawan misali a wannan zabe mai zuwa ta hanyar kin yarda a yi amfani da su. Ta kara da cewa duk wanda ya ba da gudummuwa wajen cutar da al’umma, Allah zai tambaye shi ranar Alkiyama.
Ambassador Hajiya Samira Bala Usman “Tauraruwar Kasar Hausa, Jagaban Matan Najeriya” ta yi addu’ar Allah ya sa a gudanar da yakin neman zabe da zaben 2027 cikin zaman lafiya a kowane mataki. Tana da fatan za a samu shugabanni nagari daga matakin shugaban kasa, gwamnoni, sanatoci, har zuwa ‘yan majalisun tarayya da na jaha.






