Zaɓen 2027: Dini Falalu Fagge Ya Yi Kira Ga Al’ummar Kano Ta Kudu Su Ƙara Mara Wa Sanata Kawu Sumaila Baya

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Wani matashin ɗan siyasa a jam’iyyar APC, Dini Falalu Fagge, ya yi kira ga al’ummar Kano ta Kudu da su ci gaba da bai wa Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila haɗin kai da goyon baya a zaɓen 2027 mai zuwa, domin ci gaba da amfana da ayyukan ci gaba da ake gudanarwa a yankin.

Dini Falalu ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce duk da cewa yankin Kano ta Kudu ya samu wakilcin sanatoci tsawon sama da shekaru 16, bai taɓa ganin wani Sanata da ya yi aiki tuƙuru wajen kula da ci gaban yankin kamar Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ba.

Ya bayyana cewa Sanatan ya ba da muhimmiyar gudunmawa a fannin ilimi, inda ya ɗauki nauyin ɗalibai a manyan makarantu daban-daban, tare da kafa Jami’ar Isti’qama da ke garin Sumaila.

A fannin noma kuwa, ya ce Sanata Kawu Sumaila ya samar da hanyoyin ruwa domin bunƙasa noman rani a garuruwa daban-daban na yankin, tare da raba wa manoma takin zamani da iri kyauta domin noman damina.

Bugu da ƙari, Dini Falalu ya ce Sanatan ya gina asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya, tare da samar da magunguna, domin inganta harkokin lafiya da sauƙaƙa samun kulawar lafiya ga al’ummar yankin.

Ya jaddada cewa a baya, wasu daga cikin waɗanda aka tura domin wakiltar yankin ba su bar wani abin a zo a gani ba, amma a yanzu, al’umma na amfana da wakilcin Sanata Kawu Sumaila ta hanyar ayyuka da dama, ciki har da tallafawa jama’a da ’yan siyasa da jari, da kuma rabon motocin haya da babura.

Dini Falalu Fagge ya ce: “Ina kira ga al’ummar Mazaɓar Kano ta Kudu kada ku sake wani ya zo ya yi muku daɗin baki. Ku yi amfani da abin da kuka gani da idanunku na ayyukan da Kawu Sumaila ya gudanar. Ku ƙara ba shi dama karo na biyu a zaɓen 2027 domin ci gaba da gina yankin, jihar Kano da ƙasa baki ɗaya.”

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum