Sheikh Husain Yakub Rano Ya Roƙi Masu Neman Shugabanci Su Ji Tsoron Allah

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Malamin addinin Musulunci, Sheikh Husain Yakub Rano, ya yi wani saƙo na musamman ga ’yan siyasa, masu riƙe da madafun iko da kuma masu neman shugabanci, inda ya yi kira da su ji tsoron Allah su kuma yi adalci ga al’umma.

A cikin sanarwar da ya fitar, Sheikh Rano ya ce ya kamata a gudanar da siyasa cikin mutunci, haƙuri da fahimtar juna, yau ya zama dole a tunawa masu shugabanci cewa “mulki ba ya dawwama”.

Ya ce duk tsawon shekarun da mutum zai yi a kan mulki, wata rana zai sauka. Ko dai wa’adinsa ya ƙare, wani ya zo ya maye gurbinsa; ko kuma Allah Ya karɓi ransa. Wani lokaci ma mutum yana nan yana raye yana kallo an maye gurbinsa.

“Abin da zai tsaya bayan mutum ba mulki ba ne, sai ayyukansa da tarihinsa. Saboda haka ya zama wajibi ga duk wanda Allah Ya ba amanar shugabanci ya san cewa wannan amāna ce mai girma, kuma zai yi bayani a kanta a gaban Allah,” in ji shi.

Sheikh Rano ya ce ya zama wajibi shugabanni su yi adalci tsakanin jama’a, su tausaya wa talakawa, su saurari kukan masu rauni, su kare haƙƙin waɗanda ba su da murya, kuma su yi amfani da iko wajen yi wa al’umma hidima, ba wajen zaluntarsu ko cin amanarsu ba.

Ya bayyana cewa ‘adalci shi ne babban abin da zai rage’ Ya ce shugabanci mai adalci yana da wahala kuma yana buƙatar haƙuri da tsoron Allah, amma falalarsa tana da girma. Ya tuna da hadisin da ya ce daga cikin mutanen da za su sami inuwa a ranar da babu wata inuwa sai inuwar Allah, akwai shugaba mai adalci.
Haka zalika ya yi gargadi kan zaluntar talakawa, inda ya ce Manzon Allah ya yi gargadi mai tsanani game da shugabanni da ke cutar da jama’arsu.

Malamin ya kuma ce al’umma ba za ta iya rayuwa ba tare da shugabanci ba. Saboda haka bai kamata mutanen kirki su janye daga harkokin shugabanci ba saboda sun gaji da rashin adalci. Ya ce ko dai nagari su shiga su gyara, ko kuma a bar fagen ga waɗanda ba su damu da makomar jama’a ba.

Ya ƙara da cewa makomar ƙasa na buƙatar zaman lafiya da hangen nesa. “Mu daina zargi da zagin juna. Mu rage ƙiyayya. Kowa ya zo da irin baiwar da Allah Ya ba shi ya bayar da gudummawa. Malami da iliminsa, ɗan siyasa da ikonsa, matashi da ƙarfinsa, dattijo da gogewarsa — kowa yana da rawar da zai taka,” in ji shi.

Sheikh Husain Yakub Rano ya yi addu’ar:
“Ya Allah! Ka ba mu shugabanni masu tsoronKa, masu adalci da tausayi. Ka ba mu kuma ikon zaɓar da goyon bayan duk wanda zai zama alheri ga ƙasarmu da al’ummarmu. Ka gyara Najeriya, Ka haɗa zukatan ’yan ƙasarta, Ka kuma ba mu mafita daga dukkan wahalolin da muke ciki.

  • Related Posts

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Sakamakon irin dimbin alheri da gudummawar da dan takarar majalisar tarayya na PDP, Hon. Alhaji Abubakar Ibrahim Maina, ke bai wa al’ummar karamar hukumar Tarauni, al’ummar…

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo