Daga Ibrahim Muhammad Kano
Sakataren Yaɗa Labarai na jam’iyyar PDP na Jihar Kano, Kwamared Ahmad Dauda Lawan, ya yi kira ga al’ummar jihar da su ƙara bai wa jam’iyyar goyon baya da haɗin kai domin samun nasara a zaɓen 2027.
Kwamared Lawan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce suna fatan Allah ya ba jam’iyyar nasara daga matakin ƙasa har zuwa jihohi da ƙananan hukumomi.
Ya yi kira ga al’ummar Kano da su sake zaɓar jam’iyyar PDP, yana mai cewa yawancin ci gaban da aka samu a ƙasa da jihar Kano tun daga shekarar 1999 zuwa yanzu, an samu su ne a ƙarƙashin mulkin jam’iyyar.
“Saboda haka, muna ƙara jaddada kira ga al’ummar Jihar Kano, tun daga ’yan kasuwa, dattawa, mata, matasa, ma’aikata da masu sana’o’i daban-daban, da su ƙara bai wa jam’iyyar goyon baya. Domin tasiri da karɓuwar jam’iyyar na nan daram a cikin al’umma,” in ji shi.
Kwamared Ahmad Dauda Lawan ya ce za su yi aiki tukuru wajen wayar da kan al’umma da kuma ƙara fahimtar da su cewa ƙasa da jihar Kano sun shiga wani yanayi mara daɗi. Ya ce suna fatan Allah ya dawo da PDP kan mulki domin ta kawo gyara da inganta rayuwar al’umma.
Ya bayyana cewa a yanzu jam’iyyar ta tsayar da ’yan takara tun daga majalisun dokokin jiha, Majalisar Wakilai da Majalisar Dattawa a shiyyoyi uku na Jihar Kano, tare da ɗan takarar gwamnan jihar da mataimakinsa.
Don haka, ya yi kira ga al’umma da su fito su bai wa ’yan takarar PDP goyon baya a kowane mataki domin jam’iyyar ta samu nasara a zaɓen 2027, ta dawo da tattalin arziki, inganta tsaro da kwanciyar hankali, tare da samar da hanyoyin da za su bunƙasa rayuwar al’umma.
Ya ce al’ummar Jihar Kano na marmarin dawowar jam’iyyar PDP saboda irin halin da ƙasa da jihar suka shiga na rashin jin daɗi. A cewarsa, a lokacin mulkin PDP, al’umma sun san ana samun kayan abinci cikin sauƙi, man fetur cikin sauƙi da sufuri mai sauƙi, yayin da ake samun walwala, tsaro da bunƙasar tattalin arziƙi.
Ya ƙara da cewa ya kamata al’umma su mara wa ’yan takarar PDP baya a zaɓe mai zuwa, domin jam’iyyar ta tantance tare da tsayar da nagartattun ’yan takara waɗanda, idan suka samu nasara, za su fitar da al’umma, ƙasa da jihar Kano daga ƙuncin da suka shiga.
Sakataren Yaɗa Labarai na PDP na Jihar Kano, Kwamared Ahmad Dauda Lawan, ya kuma yi kira ga malamai da dattawa da su riƙa sanya jam’iyyar PDP cikin addu’o’insu domin samun nasara. Ya ce idan jam’iyyar ta samu nasara, al’umma za su ci gaba da amfana da romon dimokuraɗiyya a5 ƙarƙashin mulkin jam’iyyar da ya bayyana a matsayin mai kyakkyawar manufa kuma babba a nahiyar Afirka.






