Mun Gamsu Da Ayyukan Ɗan Majalisar Fagge, Za Mu Ci Gaba Da Mara Masa Baya -Sani Babba

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Wani jigo a jam’iyyar APC, Sani Babba, ya bayyana gamsuwarsa da ayyukan raya ƙasa da kuma kyakkyawan wakilcin da ɗan Majalisar Dokoki ta Jihar Kano mai wakiltar ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Tukur Muhammad, ke yi.

Sani Babba ya ce ɗan majalisar ya samar da makarantu a yankin, ciki har da wata makaranta da aka gina a Dandalin Fagge, da kuma wani babban gida kusa da Gidan Sarkin Aska da ke Rijiyar Lemo, wanda ya mayar da shi makaranta da za a buɗe nan gaba kaɗan.

Ya ƙara da cewa ɗan majalisar ya gina hanyoyi, ya gyara masallatai, tare da gyara da kuma haƙa rijiyoyin burtsatse a wurare daban-daban na ƙaramar Hukumar Fagge.

A cewarsa, “Hon. Tukur Muhammad mutum ne mai sauƙin kai, mai mutunta jama’a da sauraron koke-kokensu, yana kuma ba matasa kulawa ta musamman. Ya ce dan majalisar na tallafawa iyaye mata da jarin sana’o’i, duk da cewa ba ya son a riƙa yayata irin tallafin da yake bayarwa.”

Sani Babba ya ce kasancewar gwamnatin Kano ta shigo ta tarar da su a jam’iyyar APC, tare da gamsuwarsu da ayyukan Gwamna Abba Kabir Yusuf, yanzu an zama ɗaya, lamarin da ya sa suke yaɗa manufofin gwamnatin a faɗin yankin.

Ya ce idan suka ga wani wuri da ake buƙatar aiki a Fagge, sukan sanar da Shugaban ƙaramar Hukumar Fagge, Hon. Salisu Usman Masu, wanda yake ɗaukar matakin aiwatar da ayyukan cikin gaggawa. “Saboda haka, za mu ci gaba da ba da goyon baya domin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a kowane mataki,” in ji shi.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum