Daga Ibrahim Muhammad Kano
Babban Mai Taimakawa Gwamnan Jihar Kano kan Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Alhaji Bashir Abubakar Yaro Galadima, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa ayyukan ci gaba da gwamnatinsa ke aiwatarwa a faɗin jihar.
Alhaji Galadima ya bayyana hakan ne yayin ganawa da manema labarai a Kano, inda ya ce gwamnatin APC ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba ta samar da ayyuka da suka shafi ilimi, lafiya, samar da ayyukan yi da tallafawa al’umma cikin ɗan gajeren lokacin da ta shafe a mulki.
Ya ƙara da cewa, “Muna kira ga al’ummar Jihar Kano da su ƙara bai wa Gwamna Abba Kabir Yusuf goyon baya a zaɓe mai zuwa, domin ya ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da za su kawo sauyi mai ma’ana a rayuwar jama’a.”
Babban Mai Taimakawa Gwamnan ya jaddada cewa ayyukan ci gaban da ake samu a yanzu sun isa su zama hujja ga al’umma su sake bai wa gwamnatin APC dama ta biyu.






