Hon. Bashir Yaro Galadima Ya Yaba Wa Gwamna Abba Kan Zamanantar da Kasafin Kuɗin Ƙananan Hukumomi

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Babban Mataimaki na Musamman ga Gwamnan Jihar Kano kan Ƙananan Hukumomi da Masarautu, Hon. Bashir Abubakar Yaro Galadima, ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan ƙoƙarin da yake yi wajen zamanantar da tsarin gudanar da kasafin kuɗin ƙananan hukumomi a jihar.

Hon. Galadima ya bayyana hakan ne yayin da ake gudanar da horo da bita ga ma’ajin ƙananan hukumomi da jami’an PRS na ƙananan hukumomi 44 na Jihar Kano.

Ya ce an shirya horon ne domin wayar da kan jami’an kan yadda za su gudanar da sabon tsarin kasafin kuɗi na zamani, wanda ya koma tsarin yanar gizo.

A cewarsa, taron ya samu cikakken halartar dukkan mahalarta da aka gayyata, inda suka samu damar fahimtar yadda sabon tsarin yake aiki da kuma yadda za su aiwatar da shi yadda ya kamata.

Hon. Galadima ya ce mahalarta taron sun yaba da tsare-tsaren Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf, musamman yadda gwamnatin ke aiwatar da ayyukan da suka shafi ci gaban al’ummar jihar.

“Gwamna Abba Kabir Yusuf, a duk lokacin da ya ji wani abu da zai amfani al’umma, ba ya saurarawa sai ya tabbatar an aiwatar da shi,” in ji shi.

Haka zalika, ya yaba wa Kwamishinan Ƙananan Hukumomi bisa jajircewarsa wajen ganin an inganta harkokin ƙananan hukumomi, yana mai cewa horon ya taimaka wajen fahimtar ma’anar zamanantar da kasafin kuɗi da kuma yadda za a gudanar da shi bisa sabon tsarin zamani.

Daga nan sai Hon. Bashir Yaro Galadima ya yi kira ga ma’ajin ƙananan hukumomi da su ƙara tashi tsaye wajen haɓaka tattara kuɗaɗen shiga na cikin gida, domin hakan zai taimaka wajen ƙara yawan kuɗaɗen da ƙananan hukumomi za su samu daga Gwamnatin Tarayya.

Haka kuma, ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Abba Kabir Yusuf da Kwamishinan Ƙananan Hukumomi da su samar wa shugabannin sashen PRS ababen hawa, domin su samu damar zagayawa lungu da saƙo na ƙananan hukumomi suna duba buƙatu da ayyukan da ya kamata a sanya cikin kasafin kuɗi.

Ya ce hakan zai taimaka wajen gano muhimman ayyukan da al’ummar ƙananan hukumomi ke buƙata, sannan a shigar da su cikin kasafin kuɗi domin aiwatar da su a faɗin Jihar Kano.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum