Kada A Bari APC Ta Yaudari Al’umma Da Kayan Abinci, Kuɗi Da Babura -Darma

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Jigo a tsarin NDC Kwankwasiyya a jihar Kano, Ambasada Hon. Yusuf Darma, ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da Najeriya baki ɗaya da su guji yarda jam’iyyar APC ta yaudare su ta hanyar raba musu kayan abinci, kuɗi da babura domin samun goyon bayansu a zaɓen 2027.

Hon. Darma ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ta gaza wajen inganta rayuwar al’umma da tabbatar da tsaro, yana mai cewa hakan ya jefa jama’a cikin ƙunci da talauci. Ya ce a yanzu jam’iyyar ta koma raba kuɗi da babura da sunan tallafi, wanda ya ce ana amfani da shi wajen jan hankalin talakawa domin su sake zaɓe ta a zaɓen da ke tafe.

Ya ce ya kamata al’umma su kare ‘yancinsu na zaɓe tare da tabbatar da cewa sun zaɓi shugabannin da za su kyautata rayuwarsu, su inganta tsaro da zaman lafiya.

“Ya kamata al’umma su kare ‘yancinsu, su tsaya su tabbatar sun zaɓi shugabannin da za su kyautata rayuwarsu da inganta tsaro da zaman lafiya. Domin duk abin da za a ba ka, idan ka zaɓi abin da zai ƙara jefa al’umma cikin ƙunci, rayuwa kai ma za ta shafe ka,” in ji shi.

Ambasada Hon. Yusuf Darma ya kuma yi kira ga al’ummar ƙasar nan da su zaɓi ‘yan takarar jam’iyyar NDC, ciki har da Obi da Kwankwaso, a zaɓen 2027, yana mai cewa ‘yan takarar jam’iyyar mutane ne jajirtattu kuma masu kishin ci gaban al’umma.

A matakin jihar Kano kuwa, ya bayyana tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, a matsayin ɗan takarar gwamna na NDC Kwankwasiyya, yana mai cewa mutum ne mai gaskiya da riƙon amana, wanda ya ce yana da kyakkyawan tarihin siyasa tun daga tushe da kuma kishin ci gaban al’umma.

Darma ya yi kira ga al’ummar Kano da su mara wa Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo baya, domin, a cewarsa, hakan zai taimaka wajen kawo sauyin siyasa a jihar tare da kawar da gwamnatin da ya zarga da cin amanar al’ummar Kano ta hanyar haɗa kai da jam’iyyar da ke mulki a ƙasa.

  • Related Posts

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan takarar majalisar tarayya na jam’iyyar ADC mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, Hon. Musaddik Bashir Usman Tofa, ya bayyana cewa jam’iyyar…

    Babu Wani Sauyi A ’Yan Takarar NDC Na Kano — Kwankwaso

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Jagoran Kwankwasiya kuma ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Sanata Dakta Rabiu Musa Kwankwaso, ya musanta samun wani sauyi a jerin ’yan takarar jam’iyyar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    Africa Academy Ta Yaye Ɗalibai 3,500 A Kano Da Suka Kammala Diploma A Shari’ar Musulunci

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Kamfanin Shafa’u Linnas Habal International Ya Horas Da Ƙwararru 60 Masu Maganin Gargajiya A Kano

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    Ba zai yiwu ka goyi bayan APC da wasu jam’iyyu a lokaci guda ba — Dauda Lawal ga Wike

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    ZAMFARA: A Wata Mai Zuwa Jirgin Sama Zai Fara Jigilar Fasinjoji Tsakanin Gusau Da Abuja

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano

    Ana Gudanar Da Bita Ga Ƙwararrun Masu Maganin Gargajya a Jihar Kano