Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugabar Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Sardauna, wadda ake kira da Turanci Sardauna College of Health Science and Technology, Hajiya Naja’atu Abdullahi, ta bayyana dalilan da suka sa ta kafa makarantar, ciki har da samar da damar karatu ga mata da kuma rage ƙarancin ma’aikatan lafiya a yankunan karkara.
Hajiya Naja’atu ta ce tun farko ta lura da ƙarancin mata da ma’aikatan jinya a fannin lafiya a Arewacin Najeriya, inda a lokacin da mutum ya je asibiti yake yawan ganin ma’aikatan lafiya waɗanda ba Hausawa ba.
Ta ce wannan yanayi ya sa tun suna ƙanana suka fara sha’awar aikin likita, domin a wancan lokacin ba su fahimci bambancin matakan ma’aikatan lafiya ba. Duk wanda suka ga yana ba da magani ko allura, likita kawai suke kira.
Ta ce: “Tun daga wancan lokacin muke da wannan sha’awar, har ta kai ga muka yi karatun fannin lafiya. Amma muka ga har yanzu ba a kai matakin da ake so ba, kuma akwai sauran gibi mai yawa.”
A cewarta, al’adun Hausawa musamman na Arewa na buƙatar a samu mata masu aikin lafiya da za su kula da mata, domin sukan fi samun nutsuwa idan mace ce ke duba su.
Ta ce: “Idan mace ce likita da za ta duba mace, za ka ga za ta samu natsuwa, kuma akwai abubuwan da za ta iya gaya mata ba tare da jin nauyin faɗa ba, saboda muna da al’adar kunya a Arewa.”
Hajiya Naja’atu ta ce wannan na daga cikin dalilan da suka sa makarantar ke ba mata muhimmanci wajen ɗaukar ɗalibai, inda ta ce idan aka duba jerin sunayen ɗaliban da suke ɗauka, mata suna daga cikin waɗanda suke ba wa fifiko.
Ta kuma bayyana cewa makarantar na ba da muhimmanci wajen ɗaukar ɗalibai daga yankunan karkara, saboda a cewarta, ƙananan hukumomin da ke cikin kwaryar birnin Kano suna da ɗimbin likitoci da ma’aikatan lafiya idan aka kwatanta da yankunan karkara.
Ta ce horar da matasa daga karkara na taimakawa wajen tabbatar da cewa bayan sun kammala karatu, za su koma yankunansu domin yin aiki da kuma taimaka wa al’ummominsu.
“Idan ka horar da ’yan karkara, idan sun gama karatu za su koma gida. Idan aure suka yi, za su iya yin aure a gida su zauna a gida. Ta haka ba za a samu tazarar da ake samu yanzu tsakanin birane da karkara wajen samun ma’aikatan lafiya ba,” in ji ta.
Hajiya Naja’atu ta ce Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Sardauna na daga cikin makarantu masu sauƙin kuɗin karatu, inda makarantar ke ba ɗalibai damar biyan kuɗin makaranta a hankali maimakon biyan shi gaba ɗaya lokaci guda.
Ta ce ɗalibi zai iya raba kuɗin makaranta zuwa kashi biyu ko uku a cikin shekara, gwargwadon tsarin karatun da yake yi, ko na shekara biyu ne ko na shekara uku.
Ta ƙara da cewa a lokacin bikin yaye ɗalibai da ƙaddamar da wasu ayyuka na makarantar, wasu ƙungiyoyi biyu sun bayar da guraben tallafin karatu (scholarship) ga kusan ɗalibai goma.
A cewarta, makarantar ta duba ɗaliban da suka yi nasara a jarabawar WAEC, suke da basira da ƙwazo, amma ba su da halin biyan kuɗin karatu, inda aka ba wasu daga cikinsu tallafin karatu.
Ta ce makarantar na kuma ci gaba da neman haɗin gwiwar wasu mutane da ƙungiyoyi masu taimakon al’umma domin su ɗauki nauyin karatun ɗalibai masu buƙata.
Hajiya Naja’atu ta bayyana cewa makarantu masu koyar da fannin kimiyyar lafiya suna da wasu sharudda da hukumomin da ke kula da su suke buƙatar cika kafin a ba su damar fara aiki, ciki har da samar da ɗakunan kwanan dalibai.
Ta ce hukumomin da ke da alhakin bayar da izinin gudanar da irin waɗannan makarantu kan tabbatar da cewa makarantar tana da wuraren kwanan ɗalibai, saboda ana son ɗalibai daga ƙananan hukumomin karkara su samu damar zuwa karatu cikin sauƙi.
Ta ce ƙarancin ma’aikatan lafiya a karkara na daga cikin dalilan da ya sa gwamnatoci ke ci gaba da ɗaukar ma’aikatan lafiya domin cike gibin da ake samu a wannan fanni.
Ta ƙara da cewa Gwamnatin Jihar Kano ta yanzu ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ma ta ɗauki ma’aikatan lafiya da dama domin ƙara yawan ma’aikatan da ake da su a fannin.
Darussan da Kwalejin ke Koyarwa
A nasa ɓangaren, Ambasada Anas Dahiru, wanda ke kula da tantance cancantar ɗaukar ɗalibai a Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Sardauna, ya ce zuwa yanzu makarantar na koyar da darussa da dama da suka haɗa da Community Health, Medical Laboratory, Dispensing Optician da Health Information Management (HIM).
Ya ce ɗaliban Community Health na samun horo kan ayyukan kula da lafiyar al’umma, ciki har da kula da mata masu juna biyu da taimaka wa wajen haihuwa, yayin da masu karatun Medical Laboratory ke koyon yadda ake gudanar da gwaje-gwajen lafiya.
Ambasada Anas ya ce tsarin shiga Kwalejin Kimiyyar Lafiya da Fasaha ta Sardauna ba shi da wahala ga wanda ya cika sharuddan shiga.
Ya ce mai neman gurbin karatu na buƙatar takardar shaidar WAEC ko NECO, da takardun shaidar makarantar firamare da sakandare, da kuma shaidar kasancewarsa ɗan asalin gari, sannan ya sayi fom tare da bin sauran tsare-tsare da ƙa’idojin shiga kwalejin.
Ya ƙara da cewa makarantar tana da ɗakunan kwanan dalibai na maza da na mata daban-daban, tare da kayan aiki da ake amfani da su wajen koyar da darussan kimiyyar lafiya da fasaha.








