Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAW).

Garo ya yi wannan kiran ne a daren ranar Asabar yayin da ya halartarci taron Mauludin Annabi na shekara-shekara da aka gudanar a unguwar Yakasai a Kano, inda a yayin taron ya rabawa dalibai da suka kammala karatun Alkur’ani kyautar Naira (N20,000) kowanne.

Mataimakin Gwamnan Wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a wajen taron wanda tsohon Shugaban Karamar Hukumar Birni kuma tsohon Kwamishinan Ayyuka na Musamman, Muntari Ishaq Yakasai, ya shirya.

Garo ya ce muhimmancin taron Mauludi ya wuce biki kawai, inda ya bukaci Musulmi da su aikata koyarwar Annabi da kyawawan dabi’unsa a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya ce rayuwar Annabi ta kasance misali ne na gaskiya, tsoron Allah, tausayi da kuma biyayya ga iyaye, inda ya bukaci Musulmi da su rike wadannan dabi’u, su nuna tausayi ga makobtansu tare da bayar da sadaka.

Mataimakin Gwamnan ya kara da cewa bin koyarwar Annabi zai kawo nasara a duniya da lahira.

Ya yaba wa Hon.Muktar Ishaq Yakasai bisa ci gaba da gudanar da taron Mauludin na shekara-shekara, wanda ya ce ya kasance al’ada ta iyali da ta shafe sama da shekaru 30.

Garo ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da baiwa iyalin karfi da arziki domin ci gaba da wannan al’ada har zuwa zamani masu zuwa.

Da yake jawabi Hon Muktar Ishaq Yakasai, ya gode wa Mataimakin Gwamnan bisa halartar taron, yana mai cewa Malaman addinin Musulunci sun jaddada muhimmancin neman ilimi kan yadda ake girmamawa da mutunta Annabi Muhammad (SAW). Ya ce yada irin wannan ilimi da zurfafa fahimta kan matsayi da koyarwar Annabi na daga cikin dalilan shirya taron na shekara-shekara.

  • Related Posts

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    DAF Ta Gudanar da Bikin Karrama Zakakuran Mutane 10 ‘Yan asalin Dawakin Tofa da Suka Gabata Bisa Gudunmuwa da Suka Bayar

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ƙungiyar Dawakin Tofa Academic Forum (DAF) ta gudanar da bikin karrama zakakuran mutane 10 da suka gabata, bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength