Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu.
Da yake bayani kan kafuwar makarantar, Malam Khalid Shu’aibu Khalid, wanda shi ne ya assasa ta, ya ce ya samar da Makarantar Al-Burhan ne a shekarar 2017 a wani bigire na gidansa.
Daga baya suka samu matsuguni suka tare a shekarar 2012 a bayan WRECA, Goron Dutse, inda ya ci gaba da gudanar da makarantar.
Ya ce ya soma gudanar da makarantar da malamai uku da dalibai 30, wanda a yanzu suna da yawan dalibai 250.
Ya ce karo na hudu kenan da suke bikin saukar karatun. A karon farko dalibai 28 ne, na biyu dalibai 24, na uku dalibai 32, wannan karo na hudu kuma dalibai 13 ne. Adadin ya ragu ne saboda sun tsananta wajen tantance karatun.
Ya ce daliban da farko su 22 ne da aka tantance karatunsu aka samu 13, kuma duk cikin wadanda suka yi sauka kowanne yana da ingantacciyar haddar Al-Qur’ani.
Malam Khalid Shu’aibu Khalid yace kalubalen da suke fuskanta bai wuce na sauran makarantu ba, kuma suna da kyakyawar alaka da iyaye.
Shima daya daga cikin iyayen daliban, wanda ‘yarsa ke cikin wadanda suka yi saukar haddar, Alhaji Abubakar Usman, ya bayyana farin cikinsa tare da yabawa kokarin makarantar.
Yace za su ci gaba da baiwa makarantar gudummawa, kuma wannan haddar da ‘yarsa ta yi, zai ba ta rago, ko ya yi mata gagarumar walima saboda farin cikin wannan haddar da ta samu ta Al-Qur’ani juzu’i 60.








