Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027, harkokin siyasar jihar Kano na ƙara ɗaukar sabon salo, inda hankalin al’umma ke karkata kan irin jagorancin da jihar ke buƙata.
Ɗaya daga cikin sunayen da ke ƙara fitowa fili a wannan tattaunawa shi ne Hon. Isa Nuhu Isa Ɗanfulani, ɗan takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Zenith Labour Party (ZLP), wanda ya ɗauki taken siyasa mai cewa: “Adalci, Daidaito da Ci gaba.”
Masu nazarin siyasa na ganin takarar Ɗanfulani ba wai kawai neman muƙami ba ce, illa ƙoƙari ne na gabatar da sabon tunani kan yadda za a magance matsalolin tattalin arziƙi da zamantakewar da suka addabi jihar.
A cewar wata takarda da tawagar Ɗanfulani ta fitar, babbar tambayar da ke gaban al’ummar Kano a yau ita ce: Wane irin tattalin arziƙi Kano za ta gina? Ta yaya za a mayar da miliyoyin matasanta masu bayar da gudunmawa ga tattalin arziƙi? Kuma ta yaya noma, ilimi da kasuwanci za su zama ginshiƙan ci gaba na gaskiya?
Dan takarar ya bayyana cewa manufarsa ta ginu ne a kan ginshiƙai uku: Daidaito, wajen rabon dama da jarin gwamnati; Adalci, ta hanyar mutunta doka da cibiyoyi; da kuma Ci gaba, wanda talaka zai gani kuma ya ji tasirinsa a rayuwarsa ta yau da kullum.
A fannin tattalin arziƙi, Ɗanfulani na ganin cewa babbar dukiyar Kano ita ce al’ummarta. Don haka, ya ce ya kamata a mayar da hankali wajen bunƙasa fasaha, kasuwanci, ƙirƙire-ƙirƙire da masana’antu, domin matasa su zama masu samar da ayyukan yi, maimakon masu neman aiki kawai.
Haka zalika, ya yi nuni da muhimmancin mayar da noma ya zama kasuwanci na zamani, ta hanyar zuba jari a ban ruwa, ajiya da sarrafa amfanin gona, tare da haɗa manoma kai tsaye da masana’antu da kasuwanni.
Dangane da ilimi kuwa, ya ce Kano ta gobe za ta fafata da manyan biranen duniya, don haka dole ne a ɗauki ilimi a matsayin zuba jari ga makoma, ba kashe kuɗi kawai ba, ta hanyar shirya matasa don fafatawa a fannonin kimiyya, fasahar zamani da tattalin arzikin dijital.
Ɗanfulani ya kuma jaddada cewa babu ci gaba ba tare da tsaro ba, inda ya ce dole ne a samar da yanayin da manomi zai je gonarsa cikin aminci, ɗan kasuwa ya gudanar da harkokinsa cikin kwanciyar hankali, sannan mai zuba jari ya samu kwarin gwiwar gudanar da harkokinsa.
A ƙarshe, ya ce gwamnatin da yake son kafawa za ta kasance gwamnati mai gaskiya da riƙon amana, wadda ’yan ƙasa za su iya auna ayyukanta ta hanyar tambayoyi uku: Me aka yi alƙawari? Me aka cika? Kuma wa ya amfana?
Ya ce zaɓen 2027 a Kano bai kamata ya zama gasar mutane kawai ba, sai dai ya zama gasar ra’ayoyi da tsare-tsare masu amfani ga al’umma.






