ADC Ce Mafita Ga Jihar Kano -Hon. Musaddik Tofa

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ɗan takarar majalisar tarayya na jam’iyyar ADC mai wakiltar ƙananan hukumomin Dawakin Tofa, Tofa da Rimin Gado, Hon. Musaddik Bashir Usman Tofa, ya bayyana cewa jam’iyyar ADC na ƙara samun karɓuwa a faɗin ƙasar nan, musamman a jihar Kano da yankin mazaɓarsa.

Hon. Musaddik ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Kano, inda ya ce halin da ake ciki a ƙasar na buƙatar sauyi, kuma jam’iyyar ADC na daga cikin jam’iyyun adawa da ake ganin suna da tasiri wajen neman wannan sauyi.

Ya ce yanayin da ake ciki a yanzu na buƙatar kowane ɗan ƙasa ya yi tunani mai zurfi kan makomar kansa, iyalinsa da al’umma baki ɗaya, domin babu wani mai hankali da zai so ’yan uwansa da ’ya’yansa su ci gaba da rayuwa cikin mawuyacin hali.

A cewarsa, ADC jam’iyya ce da ta sanya samar da mafita ga al’umma cikin manufofinta, ciki har da samar da guraben aikin yi ga matasa da kuma ƙoƙarin tabbatar da cewa ta tsaya kan manufofin da aka kafa ta a kansu.

Hon. Musaddik ya ƙara da cewa abin da yake ƙarfafa wa al’umma gwiwa a duk lokacin da suke tunkarar zaɓe shi ne su guji yin tunanin kansu kawai, su kuma duba abin da zai amfani sauran ’yan ƙasa.

Ya ce bai kamata mutum ya zaɓi ɗan takara saboda kawai yana da wata mu’amala ta musamman da shi ko kuma yana ganin zai samu wata fa’ida ta kansa ba. A maimakon haka, ya kamata mai zaɓe ya yi tunanin ’yan uwansa, maƙwabtansa da sauran al’umma waɗanda ba su da wata alaƙa ta kai tsaye da ɗan takarar.

“Idan kai ka samu mafita, su ma sun samu mafita? Idan mutum ya yi irin wannan tunanin, zai taimaka masa wajen yin zaɓin da ya dace,” in ji shi.

Ya ce a nasa nazarin, jam’iyyar ADC ce za ta iya samar da irin wannan mafita ga al’umma.

Da yake magana kan zargin matsin lamba ga jam’iyyun adawa, Hon. Musaddik ya ce jam’iyyar mai mulki na ƙoƙarin dakile ayyukan jam’iyyun hamayya saboda ganin irin tasirin da ADC ke samu, musamman a jihar Kano.

Ya yi zargin cewa an cire allunan tallan wasu ’yan takarar ADC, ciki har da nasa, yana mai cewa irin wannan mataki na iya hana jam’iyyun adawa samun damar bayyana manufofinsu ga jama’a.

Ya ce lamarin bai taƙaita ga jihar Kano kaɗai ba, yana zargin cewa a faɗin ƙasar ana ƙoƙarin taƙaita damar jam’iyyun adawa wajen gudanar da harkokinsu.

Hon. Musaddik ya ce duk da cewa gwamnatin jihar Kano ta musanta hannu a lamarin, su na da hujjojin da ke nuna cewa an umurci kamfanin da ya sanya tallan ’yan takarar ADC da ya cire su.

A cewarsa, an kuma yi barazanar janye lasisin kamfanin na yin tallace-tallace a Kano idan bai cire allunan ba, abin da ya ce yana nuna cewa akwai ƙoƙarin hana jam’iyyar hamayya bayyana kanta ga jama’a.

Ya ƙara da cewa abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda wasu shugabanni ke manta da abubuwan da suka faru da su a baya. Ya yi nuni da cewa shi da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, sun taɓa kasancewa cikin tafiyar NNPP, inda ya ce ya ba gwamnan gudunmawa a lokacin da suke tare da shi da Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.

Hon. Musaddik ya ce abin mamaki ne yadda mutum zai manta da abubuwan da suka faru a baya, musamman irin matsalolin da suka fuskanta a lokacin zaɓen 2019, inda ya ce wasu masu riƙe da gwamnati a lokacin suka yi ƙoƙarin danne tafiyarsu.

Ya ce ya kamata shugabanni su riƙa tuna irin abubuwan da suka faru da su a baya, su kuma yi ƙoƙarin kauce wa maimaita abin da suka taɓa ganin bai dace ba.

“Shugaba ya kamata ya kasance shi ne kan gaba wajen misalta adalci da kyawawan ɗabi’u. Ya kamata ya zama abin koyi wajen yin abin da ya dace, ba wai a riƙa ganin ana maimaita abubuwan da ba su dace ba,” in ji shi.

A ƙarshe, Hon. Musaddik Bashir Tofa ya ce a matsayinsu na Musulmi, sun yi imanin cewa wajibi ne su tsaya kan gaskiya da neman gyara, yana mai cewa sun yi imanin Allah na tare da masu neman gaskiya da gyara.

Ya ce babu wani abu da za a yi da zai karya musu gwiwa ko ya sa su daina fafutukar ganin jam’iyyar ADC ta samu nasara a matakai daban-daban na zaɓe.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum