Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Dan takarar Majalisar Jiha a ƙaramar Hukumar Gwale ƙarƙashin jam’iyyar ADP mai alamar littafi, Dakta Bashir Aliyu (Basirun OC), ya ƙaddamar da gagarumin gangamin feshin maganin sauro a yankin Ɗorayi, domin yaƙar cutar zazzaɓin cizon sauro (Malaria) a fadin ƙaramar hukumar Gwale da ke jihar kano.
Da yake jawabi bayan ƙaddamar da shirin, Dakta Bashir Aliyu ya bayyana cewa wannan mataki na farko ne daga cikin shirye-shiryensa na inganta harkar lafiya a Gwale.
Ya ƙara da cewa akwai wasu muhimman shirye-shirye da zai bijiro da su nan gaba kaɗan, waɗanda suka hada da:
1. Samar da magungunan zazzabin cizon sauro (Malaria) kyauta,
2. Samar da magungunan hawan jini,
3. Samar da isassun magunguna a asibitocin dake fadin Karamar Hukumar Gwale da dai sauransu.
Dakta Bashir Aliyu “Basirun OC” ya jaddada cewa suna da manufofi masu yawa da za su amfani al’ummar Gwale, domin suna zaune a cikinsu kuma sun san matsalolin da suke fuskanta. Ya ce da yardar Allah, idan ya samu dama zai magance wadannan matsaloli gaba daya.






