DAF Ta Gudanar da Bikin Karrama Zakakuran Mutane 10 ‘Yan asalin Dawakin Tofa da Suka Gabata Bisa Gudunmuwa da Suka Bayar

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar Dawakin Tofa Academic Forum (DAF) ta gudanar da bikin karrama zakakuran mutane 10 da suka gabata, bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ci gaban yankin.

Taron, wanda ya gudana a ɗakin taro na Gidan Mumbayya ranar Asabar, ya samu halartar ɗimbin ‘yan asalin yankin.

Da yake jawabi a taron, Shugaban ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Hon. Anas Muktar Bello Ɗanmaliki, ya bayyana farin cikinsa bisa wannan tunani da Dawakin Tofa Academic Forum ta yi na shirya taron da aka girmama iyaye a lokacinsa, wanda kamata ya yi ace Karamar Hukuma ce ta yi.

Yace, “Muna kira wannan irin taro ya zama na duk shekara, inda za a riƙa ɗauko mutane da suka gabata da kuma waɗanda ke raye, ‘yan asalin yankin, da suka bada gudunmawa ga Dawakin Tofa da jihar Kano ana karrama su.”

Ya kuma bayar da shawarar a riƙa gudanar da taron a ƙaramar hukumar, hakan zai ba da damar mutane da yawa su sami halarta, tare da alƙawarin ba da dukkan gudunmawa domin nasarar gudanar da taron.

A yayin taron, Hon. Anas Muktar Bello Ɗanmaliki ya bayyana bayar da tallafin kuɗi ga iyalan mutane 10 da aka karrama a taron na N10m kowane gida zai sami N1m

Hajiya Jamila Magaji Abdullahi, Akanta Janar ta Jihar Kano, wadda aka karrama mahaifinta, marigayi tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Magaji Abdullahi, ta shaida wa ‘yan jarida cewa
Wannan rana ce ta farin ciki a gare su, ba abinda za su yi sai godiya ga Allah da suka ga wannan lokaci, da kungiyar Dawakin Tofa Academic Forum ta yi wani abu na farin ciki da za su yi alfahari da shi, suna kuma yi musu godiya akai da duk wadanda suka zo taron.

Ta kara da cewa, suna matukar alfahari da irin ayyukan da mahaifinsu ya yi, suma za su yi iya bakin kokarinsu mu ga sun dora akan abin da ya yi da yardar Allah.” Ta kara godiya ga Dawakin Tofa Academic Forum akan wannan karamci da suka yi musu.

Farfesa Aishatu Abdu Isma’il, wadda ta fito daga iyalen gidan tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Audu Dawakin Tofa, ta ce, “Babu abin da za mu ce da wannan ƙungiya da ta karrama mutanen da suka yi aiki tukuru wajen kawo ci gaban Dawakin Tofa. Muna fatan wannan ya zama hanya, da na baya za su yi koyi da shi. A adana tarihi ya zama mai amfani, wanda za a koyawa na baya riƙo da gaskiya da amana da jajircewa da taimakawa al’umma. Wannan zai sa Dawakin Tofa da Kano da Najeriya za su ci gaba da habaka.”

Farfesa Aishatu Abdu Isma’il ta ƙara da cewa, Darasi da suka ɗauka shi ne, mahaifinsu marigayi Alhaji Audu Dawakin Tofa yana yawan koya musu tsayuwa akan gaskiya da riƙon amana. Ana yawan ce mishi a wajen aiki baya gajiya. Wannan darasi muka ɗauka, duk lokacin da aka ba ka aiki, ka ɗauka amana ce. Saboda haka sai ka sauke amanar tun daga farko har ƙarshe, ba ka yi aiki kawai rabi da rabi ba ko na son rai ba. Idan aka koma baya a kalli yadda na ba ya suka yi aiki, a duk waɗanda aka karrama a taron, mutum 10 da aka faɗa, sun yi aiki da gaskiya, sun zaburar da na baya. Irin wannan ya kamata mu ɗauka a matsayin ginshiƙi a kan abin da za mu ɗora a kai.”

Shima da yake zantawa da ‘yan jarida, Farfesa Nura Yaro Dawakin Tofa ya ce: “Bayyana taron da cewa na tunawa da girmamawa da martabawa da karrama mutane da suka yi rayuwa a Dawakin Tofa, suka ba da gudunmawa da yanzu ba sa duniya, shi ne aka shirya wannan taro dan a tuna da su, a karrama su.

Ya ce, “Wannan abu ne da yake nuna, wanda ya bai wa al’umma gudunmawa ana sane da shi. Wannan kamar wani abu ne da zai sa mutane na yanzu su jajirce wajen ba da gudunmawa ga al’ummarsu, domin in ba sa duniya za a tuna da alkhairin da suka yi.”

Farfesa Nura Yaro Dawakin Tofa ya ce waɗanda aka karrama an zaɓo su ne bisa cancanta, kasancewar gudunmawa da suka bai wa Najeriya, Arewa, Jihar Kano da kuma Karamar Hukumar Dawakin Tofa.

Da yake bayani game da taron Shugaban Dawakin Tofa Academic Forum, Dakta Junaid Ɗanladi, ya bayyana cewa, “An ƙirƙiri taron ne domin su tuna da iyaye gwarzaye na Karamar Hukumar Dawakin Tofa bisa gudunmawar da suka bayar na ci gaban yankin da Jihar Kano da kasa baki daya, domin tunawa da su da yi musu addu’a. Mutane na wannan zamani za su yi koyi da abubuwan da suka yi, kuma zai nuna mana cewa idan mutum ya yi abin alkhairi yana raye ko baya raye, akwai ranar da zata iya zuwa a tuna da shi.”

Dakta Junaid Ɗanladi ya ce burinsu a wannan ƙungiya da suka kafa a matsayinsu na malamai a manyan makarantu, shi ne domin su ga sun inganta ilimi a karamar hukumar Dawakin Tofa, domin gwamnati kaɗai ba za ta iya gamsarwa ba. Ana buƙatar shigowar musamman kungiyoyi irin nasu na masana da sauran bangarori domin ganin an sami hadin kai da ci gaba a Dawakin Tofa.
Shima tsohon Shugaban Dawakin Tofa Academic Forum, Dakta Amir Abdu’azez, ya ce duba da irin yanayi da wannan zamani ake ciki na manta alkhairi, daga an yi abin alkhairi sai a manta, amma idan aka yi akasin haka sai a ji ana ta ba za shi, sai muka ga cewa duk wata nasara da aka gani an samu, wasu ne suka yi wata shimfida a baya, wanda bai kamata a manta da su ba, ya kamata a tuna da su.”

Ya ce, “Tunawa da mutane akan abinda sukayi na alkhairi ba sai suna da tarin dukiya ko tarin mukamai ko tarin wani abu na duniya ba. In aka duba gudummuwa da suka bayar a rayuwa koda shekaru sukayi da rasuwa, dole abin da suka yi a zo a gode musu, a yi musu addu’a, a karrama su akai
Yace, “Kusan mutane guda 10 da aka karrama, akwai wasu daga cikin su, su suka kafa Karamar Hukumar Dawakin Tofa, kamar Madaki Bello, tun kafin ayi tsarin kananan hukumomi, tun Dawakin Tofa tana gunduma, ya zo a matsayin Hakimi ya shugabanceta. Duk wani abu da ake takama da shi, irin makarantu na farko, shi ya yi su.
Dakta Amir Abdu’azez yace, “Mutane kamar marigayi Alhaji Adamu Danguguwa, wanda aka bashi shugabancin karamar hukimar na farko, duk wani abu da ake nema a yiwa Karamar Hukuma, shi ya assasa shi, shi ya kawo harkar ma’aikata, ya gina ta daga tushe. Wasu da suka biyo baya suka dora, kamar marigayi Ahmad Isma’il Dungurawa, da shine ya gina sakatariya, kuma ya yi Dan Majalisa. Ga kuma manya-manya irinsu marigayi Audu Dawakin Tofa, wanda Jihar Kano suka jagoranta, suka yi mata hidima, ga irinsu marigayi Malam Alasan Dawaki, ga irinsu marigayi Injinaiya Magaji Abdullahi, wanda duk kasarnan an san shi, ya rike mukamai daban-daban. Yana daga cikin injiniyoyi na farko a Kano, tun lokacin Audu Bako, sun yi abubuwa da yawa.”
Cikin manyan iyaye da suka halarci taron sukayi bayani akwai Saveya Nadu Yahaya da Madakin Kano hakimin Dawakin Tofa Yusuf Nabahani.

  • Related Posts

    Mataimakin Gwamnan Kano Ya Halarci Taron Maulidin Manzo (S) da Hon. Muktar Ishaq Ya Saba Shiryawa A Yakasai

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Kwamared Murtala Sule Garo, ya yi kira ga al’ummar Musulmi, musamman matasa, da su yi koyi da rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad…

    Iyayen Yara Sun Yaba Wa Makarantar Al-Burhan International College Bisa Yaye Mahaddata Al-Qur’ani Karo Na Huɗu

    Daga Ibrahim Muhammad, Kano Makarantar Al-Burhan International College da ke Bayan Wailaki a Jihar Kano, ta gudanar da bikin yaye mahaddata Al-Qur’ani karo na hudu. Da yake bayani kan kafuwar…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength