Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Shugabar cibiyar Kano LEAD, Barista Aisha Ɗankani, ta bayyana cewa ya kamata jihar Kano ta kasance kan gaba a Najeriya wajen yawan masu katin zaɓe, duba da yawan al’ummar da take da su. Sai dai ta ce sakacin al’umma ya sa adadin masu katin zaɓe a jihar bai wuce miliyan shida da ɗoriya ba.
Barista Aisha ta bayyana hakan ne yayin wata hira da ’yan jarida a wajen taron wayar da kan mata kan sayen hannun jari a matatar man Ɗangote, wanda ƙungiyar NASSI ta shirya a Kano.
Ta ce, “Ya kamata a ce jihar Kano ta fi kowace jiha yawan masu katin zaɓe a ƙasar nan, domin ita ce jiha mafi yawan al’umma. Amma saboda sakaci, sai ga shi adadin masu katin zaɓe bai wuce miliyan shida da ɗoriya ba.”
Ta ƙara da cewa aikin da Kano LEAD ke gudanarwa shi ne zaburar da al’umma a matakin ƙananan hukumomi, tare da tattara bayanai domin tantance ’yan asalin Kano da kuma mutanen da ke zaune a jihar.
Dangane da shirin sayar da hannun jarin matatar man Dangote, Barista Aisha ta ce sun shiga cikin shirin ne saboda muhimmancin da aka ba mata, ta hanyar samar musu da damar mallakar hannun jari a matatar.
Ta jaddada cewa ƙarfafa mata ta fuskar tattalin arziki na daga cikin manyan manufofin cibiyar, inda ta bayyana muhimmancin samar musu da damarmakin da za su taimaka wajen inganta rayuwarsu da kuma samun ‘yancin kai na tattalin arziƙi.






