Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya gabatar da kasafin kudin shekarar 2027 mai kimanin Naira Tiriliyan 1.107 ga Majalisar Dokokin jihar Kano, inda ya ba ayyukan cigaba da raya karkara fifiko.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar Kano, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Talata.

Kasafin kudin mai taken”Kasafin Karfafa Nasarori da Hanzarta Raya Karkara” ya kai jimillarNaira Tiriliyan 1,107,024,004,244.48 kuma shi ne kasafin kudi na hudu kuma na karshe a wa’adin mulki na farko na gwamnatin.

Da yake gabatar da kasafin, Dawakin Tofa ya bayyana cewa Gwamna Yusuf ya ce an tsara kasafin ne domin karfafa nasarorin da aka samu tun daga shekarar 2023, kammala manyan ayyuka, da kuma karfafa muhimman ayyukan gwamnati kafin karewar wa’adin mulki na farko a ranar 29 ga Mayu, 2027.

A cewar sanarwar, an ware Naira Biliyan 693.47 (kashi 63%) domin ayyukan cigaba (Capital Expenditure), yayin da aka ware Naira Biliyan 413.55 (kashi 37%) domin kashe kudaden yau da kullum (Recurrent Expenditure).

Sunusi Bature ya ce, yawan kasafin da aka ware wa ayyukan cigaba ya nuna kudirin gwamnatin na fadada ayyukan more rayuwa, habaka jarin dan Adam da kuma zuba jarin da zai bunkasa tattalin arziki.

Ya kara da cewa jihar na sa ran samun kudaden shiga na yau da kullum har Naira Biliyan 692.64, wanda ya kunshi Naira Biliyan 142.84 daga kudaden shiga na cikin gida (IGR) da kuma Naira Biliyan 549.80 daga Asusun Tarayya.

Dawakin Tofa ya ce Gwamna Yusuf ya kuma bayyana cewa sama da kashi 90 cikin 100 na shirye-shirye, ayyuka da manufofin da ke cikin tsarin cigaban gwamnatin an cimma su.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta karfafa sa ido kan kasafin kudi, gaskiya da rikon amana domin tabbatar da ingantaccen aiwatarwa da amfani da kudi yadda ya dace.

Bayan haka ne Gwamnan ya mika Kudirin Dokar Kasafin Kudin na 2027 ga Majalisar Dokokin Jihar domin tantancewa da zartar da shi zuwa doka.

  • Related Posts

    Takarar Majalisar Jaha Da Nake A ADP Amsa Kiran Al’ummar Gwale Ne -Dakta Bashir Aliyu Galadanci

    Dag Ibrahim Muhammad Kano Dan takarar majalisar dokokin Jihar Kano a Karamar Hukumar Gwale a jam’iyyar ADP, Dakta Bashir Aliyu Galadanci, ya bayyana cewa al’ummar karamar hukumar ne suka matsa…

    INEC Ta Tabbatar Da Nafiu Sankara A Matsayin Dan Takarar Sanatan Kano Ta Tsakiya

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sunan Dakta Nafiu Sankara a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar PDP…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength