Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sunan Dakta Nafiu Sankara a matsayin ɗan takarar Sanatan Kano ta Tsakiya na Jam’iyyar PDP a zaɓen 2027.
INEC ta fitar da jerin sunayen ƙarshe na ’yan takarar da za su fafata a zaɓen, inda sunan Dakta Nafiu Sankara ya kasance cikin jerin ’yan takarar kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya.
Dakta Nafiu Sankara na daga cikin matasan da suka samu nasarar samun tikitin takarar sanata a ƙarƙashin tutar Jam’iyyar PDP, a wani mataki da ake kallon zai ba matasa damar taka muhimmiyar rawa a siyasar ƙasar.
A zaɓen da ke tafe, Nafiu Sankara zai fafata da wasu fitattun ’yan siyasa, ciki har da tsofaffin ’yan siyasa daga jam’iyyun adawa, domin neman kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya.







