Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Babban Daraktan Cibiyar Kula da Nagartar Ayyuka ta Kasa (NPC), Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi, ya dauki nauyin tarbiyantar da matasa 156 tare da koya musu sana’o’in dogaro da kai, karkashin Kungiyar Gyara Kayanka ta Kofar Dan’agundi.

An kaddamar da shirin ne a ranar Asabar a Kano, a wani taro da ya samu halartar manyan baki, jami’an tsaro, limamai, masu unguwanni da iyaye.

Da yake jawabi a wajen kaddamarwar, Dr. Baffa Babba ya ce manufar shirin ita ce inganta tarbiyyar matasa da kuma koya musu sana’o’i, kasuwanci da sauran hanyoyin samun abin dogaro da kai, domin rage matsalolin zamantakewa, ciki har da zaman banza da shaye-shaye.

Ya bayyana cewa wadanda aka zaba za su yi horo na watanni uku zuwa shida, a kan sana’o’in da suka zaba. A yayin horon, za a rika ba su kudin mota da na abinci domin saukaka musu halarta. Bayan sun kammala kuma, za a ba su kayan aiki da jari da wuraren sana’a domin su fara dogaro da kansu.

Game da kudin shirin, Dr. Baffa ya ce shi da kansa ya bayar da Naira miliyan 30,000,000, yayin da Alhaji Sani Mustapha Kurmawa ya bayar da Naira miliyan 2,000,000, Alhaji Ali Amiru kuma ya bayar da Naira miliyan 5,000,000, wanda ya kawo jimillar kudin zuwa Naira miliyan 37,000,000.

Ya jaddada cewa shirin babu siyasa a ciki. Ya ce wadanda aka zaba sun fito ne daga mabambantan tsarin siyasa, wasu kuma ba sa siyasa, kuma shi a tsarin unguwa bai taba hada siyasa da aikin cigaban al’umma ba.

Sana’o’in da za a koyar sun hada da Aluminum, Dinki, Walda, Aikin Kafinta, Gyaran Tayoyi, Sana’ar Gawayi, Kasuwancin kayan sawa, sayar da man girki, Lemun Kwalba da kuma Kananikancin Motoci.

Daga cikin wadanda suka halarci taron akwai Barrister Muhyi Magaji Rimin Gado, Shugaban Kwamitin Kar-ta-Kwana na yaki da miyagun kwayoyi na Jihar Kano, Shehin Malami dan siyasa, Ibrahim Khalil, wakilan NDLEA, Civil Defence, ‘Yan Sanda da DSS, da kuma Limamai da masu unguwanni na Dan’agundi.

A nasa jawabin, Zababben Kansilan Mazabar Dan’agundi, Hon. Ibrahim Adamu Hassan (Eka), ya yaba wa Dr. Baffa Babba, inda ya ce mutum ne mai kishin unguwar Dan’agundi. Ya ce a baya duk wata fitina sai a ce Dan’agundi, amma da aka tashi tsaye da Kungiyar Gyara Kayanka, cikin ikon Allah an kawar da fitintinun da suke tasowa. Ya ce nan gaba Dan’agundi za ta zama abin koyi a Jihar Kano wajen samar da matasa nagartattu masu tarbiyya da aikin yi.

Shi ma Shugaban Kungiyar Gyara Kayanka na Kofar Dan’agundi, Alhaji Mustapha Adam Indabawa, ya ce makasudin kungiyar shi ne jawo matasa da suke yin abin da ba daidai ba, a dora su akan hanya ta kwarai. Ya ce kungiyar ce ta jawo Dr. Baffa Babba, wanda shi ma dan unguwar ne, inda ya amince ya dauki nauyin horar da yaran na wata shida, tare da biyan kudin zuwansu da dawowarsu da ba su kayan sana’a da jari.

Indabawa, wanda tsohon Manajan Darakta na Gidan Talabishin na Abubakar Rimi ne, ya ce tasirin shirin shi ne, duk yaron da aka horar da shi na wata shida, zai samu natsuwa da sauyi a rayuwarsa, ya zama mutum nagari.

Ya kara da cewa a da, an kan tare mahadan Kofar Dan’agundi ana kwacen wayoyi, ana fadan daba da sayar da kwaya, amma yanzu duk wanda ya san Dan’agundi zai wuce yana waya lafiya lau, ba tare da ya ga wani da wuka ba ko wurin sayar da kayan maye ba. Ya ce wannan babbar nasara ce ba ga Dan’agundi kadai ba, ga Jihar Kano gaba daya.

Game da kalubalen da kungiyar ke fuskanta, Indabawa ya ce babban kalubalensu shi ne iyaye mata, wadanda yawanci ba sa yarda dansu fitinanne ne, suna kare shi idan aka kama shi. Ya ce Dan’agundi unguwa ce ta dangi da ‘yan’uwa, amma kungiyar ta yanke shawarar rufe ido, duk wanda ya yi rashin kyautawa zai girbi abin da ya shuka.

A nasa bangaren, Alhaji Sani Muhammad Kurmawa, daya daga cikin wadanda suka bayar da gudummawa, ya ce Allah ya azurta Dan’agundi da Dr. Baffa Babba, wanda kullum aikinsa tallafawa al’umma ne, ko da kudin makaranta ne, ko rashin lafiya, ko aure, ko gyaran gida ko abinci.

Ya ce abin da ya sa shi ya bayar da Naira miliyan 2,000,000 shi ne don karfafa masa gwiwa, domin idan shi ya yi da bakin katafila, kai ma ka yi da karamin cokali gwargwadon ikon ka, Allah na kallon wanda ya yi dan Allah.

Alhaji Sani ya yi kira ga matasan da za a horar da su da su kama sana’ar su da karfin gwiwa, su dage, su rike gaskiya da amana, su yi hakuri da jajircewa, domin su samu bunkasa da rufin asiri a rayuwarsu.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Baffa Babba Ɗan’agundi Ya Ɗauki Nauyin Horas Da Matasa 156 Sana’o’in Dogaro Da Kai

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Cancantar Abubakar Maina Ta Sa Tarauni Ke Son Ya Nemi Takarar Majalisar Tarayya – Isma’il Salihu

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano