Daga Ibrahim Muhammad Kano
Alhaji Abubakar Lawan Jinjiri shugaban jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Ƙiru ya bayyana cewa ɗaruruwan magoya bayan ‘yan jam’iyyar APC ne suka dawo jam’iyyar su ta NNPP saboda gamsuwa da aƙidar kawo cigaba ta jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya bayyana haka ne da yake zantawa da ‘yan jarida a lokacin da ya jagoranci waɗanda suka sauya sheƙa yin mubaya’a ga jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso a gidansa da ke kan titin Mila.
Ya ce shi ya san yaro da jagoransu Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya tura karatu ƙasar waje alhali iyayensa ba su da kuɗin da za su biya wa kansu su je ko da Abuja, amma sai ga ɗan su ya je Indiya ya yi karatu ya zama injiniya yanzu yana aiki yana taimakon iyayensa da maƙwata da al’ummarsu.
Ya ƙara da cewa ganin irin raya cigaban al’umma da raya kasa da kyakkyawan nufi da na zuciya da Kwankwaso yake da ita ake gani a aikace a fannoni daban-daban shi ya sa mutane ke ta tururuwar shigowa cikin tsarin tafiyar Kwankwasiyya.
Ya ce ga wadanda suka shigo jam’iyyar NNPP a yanzu tsarin Kwankwasiyya duk an zama abu daya da wadanda suka samu a ciki, kuma tun daga mazaba har karamar hukuma za a yi musu adalci kamar yadda jagora ya tabbatar masu.
Alhaji Abubakar Jinjiri ya ce duk jiga-jigan ‘yan hamayya a Ƙiru suna waje daya suka zo da NNPP suka ci Sanata da dan majalisar jiha da na tarayya a yankin Ƙiru Abba Kabir Yusuf ya ci Gwamna Kwankwaso ma ya ci zaben shugaban kasa ba su taba faduwa ko akwati daya ‘yan hamayya ba sa ci dama mun fi karfinsu ba su sun mutu mushen gizaka ne.
Shi ma jagoran Kwankwasiyya na karamar hukumar Ƙiru Hon. Bello Aliyu Kiru ya ce mutum 1,673 ne suka dawo jam’iyyar NNPP daga mazabun 15 karkashin dattijai guda biyu da matashi guda daya, Alhaji Lawan Dalha shugaban dattawa na APC na Kiru da tsohon dan majalisa a jamhuriya ta biyu Alhaji Aminu Lawan Kwanar Ɗangora dattijo ne mai kyakkyawar mu’amala da ya san jiya da yau.
Ya kara da cewa akwai kuma shugaban matasa da a baya suka bi wani mutum mai son biyan buƙatar kansa sai daga baya suka farga suka dawo karkashin Mahmud Kwanar Ɗangora sune jagorori da suka jawo wadannan ɗimbin tsofaffin ‘yan APC suka dawo cikin gidan Kwankwasiyya.
Hon. Bello Aliyu Kiru ya ce akwai ma tsohon sakataren ilimi na Ƙiru Balarabe Zubairu mai hoto da tsohon sakataren mulki na karamar hukumar Kiru yanzu sun dawo gidan Injiniya Dakta Rabiu Musa Kwankwaso.






