Sani Danja Ya Zama Shugaban Ƙungiyar Haɗin Kan Hausa Ta Duniya

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Kungiyar hadin kan Hausa da Hausawa ta Duniya karkashin jagorancin shugaban ta Dakta Sa’id ta nada fitaccen jarumi a Kannywood Alhaji Sani Musa Danja a matsayin shugaban kungiyar na jihar Kano.

Kungiyar dai ta kuma nada Sheikh Alhaji Rabiu Abdullahi a matsayin shugabanta na jihar kungiyar Kaduna a taron da aka yi a ranar Lahadi a jihar Kano.

A jawabinsa shugaban kungiyar na hadin kan Hausa da Hausawa na duniya Dakta Muhammad Sa’id ya ce nadin na Alhaji Sani Musa Danja da suka yi sun yi ne bisa cancanta da irin jajircewarsu da suke ganin za su ba da gudunmawa sosai domin cimma nasarar manufofin kungiyar.

Ya ce kungiyar an kafata ne sama da shekara hudu domin hada kan Hausawa duba da cewa duk inda ka shiga a duniya za ka same shi, amma akwai raunin hadin kai a tsakani amma zuwan kungiyar ta soma hada kan Hausawa na duniya yanzu haka suna da rassa a ƙasashe kusan 50.

Dakta Muhammad Sa’id ya ce Allah ya yi wa Bahaushe daraja, amma saboda rauni na rashin kulawa da hadin kai sai ya zama ko’ina sai ya zama kara-zube, amma assasa kungiyar ta tayar da Hausawa da ga barci ana ƙoƙarin hada kai domin suna yin taruka a ƙasashen duniya daban-daban.

Ya yi kira ga al’ummar Hausawa kan cewa tafiyar kungiyar tana da alkhairi, kuma idan kana ciki duk inda ka je a duniya za ka sami dauki na duk wani abu da kake nema.

Dakta Sa’id ya ce kungiyar tana da shiri na magance matsalar gararambar da ‘ya’yan Hausawa ke yi a rika koya musu sana’oi da kula da masu karatu domin su taso su zama masu amfani a rayuwarsu.

Shi ma a nasa jawabin, shugaban kungiyar na Nijeriya, Alhaji Shitu Adamu Bargaja Talban Isa, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Sakkwatawa da Kabawa da Zamfarawa mazauna Kano da Jigawa, ya taya wadanda aka nada a matsayin shugabannin kungiyar na jihohin Kano da Kaduna murna da jan hankalinsu wajen jajircewa domin cimma manufar kungiyar wajen ganin an kare kima da martabar Hausawa a duk inda suke ta haduwa a yi aiki tare da zai kawo ci gaba.

Ita ma shugabar mata ta kungiyar ta kasa, Hajiya Sa’adatu Umar Yola ta bayyana farin cikin ta bisa nadin da akayi na shugabannin kungiyar na jihohin Kano da Kaduna.

Ta ce shi kansa shugaban na Kano da aka naɗa Sani Danja ta jima tana nemansa sai katsam suka hadu har ga shi an zo an nada shi a wannan matsayi saboda cancanta a wannan kungiya da suke ganin tasirin ta mai yawa wajen hada kan Hausawa da ake samun ci gaba sosai ana hada kan Hausawa a kasashen duniya.

Hajiya Sa’adatu Umar Yola Garkuwar Kwankwaso ta ce suna da buri da tsari na taimakawa magance gararambar yara ƙanana a kan tituna dan ba su kyakkyawar tarbiyya ta koya musu sana’a da mayar dasu makaranta.

Shi ma a nasa jawabin bayan mika masa shaida na zama shugaban kungiyar hadin kan Hausa da Hausawa reshen jihar Kano, Alhaji Sani Musa Danja ya bayyana cewa duk lokacinsa aka kira ka aka ce kazo ka yi wani abu ana nuna kana da wata kima na mutumtaka da rawar da za ka taka har aka ga dacewar a kira a ba ka shugabanci.

Ya ce wannan wani abu ne da za ka ji dadin cewa mu’amalar ka tanada kyau, kuma sai ka sake jajircewa ka kyautata zuciyarka duk abin da ka yi da manufa mai kyau ba zai yi maka wahala ba, kuma kar ka dauka za ka sami hadin kan al’umma cikin sauki domin ko taimakon mutum za ka yi sai ka wayar masa da kai ya fahimce ka ya gane manufarka, sannan zai sami natsuwa ya yarda da kai.

Alhaji Sani Musa Danja ya ce da yardar Allah za su tsaya su jajirce domin su kai ga cimma manufofin kungiyar ta hada kan Hausawa, kuma ya nemi a daina la’akari da bambancin siyasa ko wani abu daban domin duk inda aka ce ci gaba taimako to a kawar da bambanci a amfanar da jama’a.

Shi ma a nasa jawabin sabon shugaban kungiyar na jihar Kaduna, Alhaji Abdullahi ya ce yana farin ciki da wannan matsayi da aka ba shi sun godewa Allah suna fata ya karfafe su ya sa duniyar da kungiyar a Kaduna ya zama a duk kasar nan ma kawai hannunsu wajen al’umma su amfani da kungiyar.

Sheikh Alhaji Rabiu Abdullahi ya yi nuni da cewa kamar yadda shugaban kungiyar na duniya ya jajirce su ma da suke mukarrabanta su zama jajirtattu idan suka yi aiki da gaskiya da amana don hada kan al’umma za a sami tasiri da nasara wajen taimakawa al’umma ta bangaren tarbiyya da jin dadi a zamantakewa tsakanin Hausawa.

Taron dai ya sami halartar shugabannin kungiyar da dama da suka hada da na jihar Jigawa Alhaji Anas Wurno da wakilin masarautar Daura da wasu daga fitattun ‘yan wasan Hausa na kungiyar Kannywood da suka hada da T.Y.Shaba da Yakubu Muhammad da sauran fitattun jarumai.

Related Posts

Rasuwar Audu Manaja Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Nijeriya -Sulaiman Hussain

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana rasuwar fitaccen ɗan kasuwa a harƙar man fetur, Alhaji Abdullahi Ahmad, wanda aka fi sani da Audu Manaja, a matsayin babban rashi ga Arewa…

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Wani sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar ADC reshen Jihar Kano, bayan wasu manyan jami’an jam’iyyar sun zargi jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso,…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Rasuwar Audu Manaja Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Nijeriya -Sulaiman Hussain

Rasuwar Audu Manaja Babban Rashi Ne Ga Arewa Da Nijeriya -Sulaiman Hussain

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A ADC Reshen Kano Kan Zargin Hana Waɗanda Ba ’Yan Kwankwasiyya Ba Takara

Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

Sanata Hanga Ɗan Gwagwarmayar Siyasa Ne Mai Neman Sauyi Da Ci Gaban Al’umma – Maikarfi Dala

Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

Asibitin Ƙashi Na Dala Ya Karrama Hon. Abba Kabir Bichi Kan Gudummawar Da Yake Bayarwa

Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

Gidauniyar NNPCL Ta Miƙa Na’urar MRI Ta Zamani Ga Asibitin Ƙashi Na Dala

LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala

LEON Projects Ta Sami Lambar Karramawa Kan Aikin Gina Ɗakin MRI A Asibitin Ƙashi Na Dala