Al’ummar Ƙaura Goje Sun Gudanar da Bikin Murnar Naɗin Sabon Dagaci

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Al’ummar Ƙaura Goje da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa a jihar Kano, sun gudanar da gagarumin biki domin taya sabon Dagacin Ƙaura Goje, Alhaji Ali Ado, murnar naɗin da Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, ya yi masa.

An gudanar da taron ne ranar Asabar a harabar Makarantar Ahmadiyya, inda mutane daga sassa daban-daban suka halarta.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan Ɓoye, wanda ya halarci taron, ya bayyana farin cikinsa da samun wannan sarauta a lokacin mulkinsa, inda aka naɗa ɗaya daga cikin ’ya’yan yankin Ƙaura Goje a matsayin Dagaci.

Ya ce ba abin da za su ce face godiya ga Allah bisa wannan babbar baiwa da ya yi musu, musamman ganin cewa a lokacin da yake jagorantar ƙaramar hukumar ne aka naɗa ɗan yankin a matsayin Dagaci.

Hon. Yusuf Imam Ogan Ɓoye ya kuma gode wa Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, wanda ya ce ta dalilinsa ne ya zama zaɓaɓɓen Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa, sannan kuma aka samu wannan ci gaba da aka shafe shekaru ana nema.

Ya kuma miƙa godiyarsa ga Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, da dukkan ’yan majalisarsa, Hakiman Nasarawa da na Gunduma, Dagatai, sauran al’umma, magoya baya da duk waɗanda suka bayar da gudunmawa ta kowace hanya, musamman addu’o’in da suka taimaka wajen ganin an cimma wannan buri.

Ogan Ɓoye ya bayyana matuƙar godiyarsa ga Dagacin Gama bisa irin gudunmawa da goyon bayan da ya bayar wajen tabbatar da wannan al’amari. Ya kuma taya sabon Dagacin murna tare da addu’ar Allah Ya ba shi ikon gudanar da mulkinsa cikin adalci da zaman lafiya.

Shi ma sabon Dagacin Ƙaura Goje, Alhaji Ali Ado, ya gode wa dukkan waɗanda suka taka rawa wajen ganin wannan sarauta ta tabbata, tare da roƙon Allah Ya ba shi ikon sauke nauyin da aka ɗora masa cikin adalci.

Dagacin Ƙaura Goje ya gode wa Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Yusuf Imam Ogan Ɓoye, bisa ƙoƙarin da ya yi wajen ganin an cimma wannan nasara. Ya kuma gode wa Mai Martaba Sarkin Kano, Khalifa Muhammad Sanusi II, bisa wannan karamci da Masarautar Kano ta yi masa, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da biyayya ga masarauta da kare martabarta.

Ya kuma miƙa godiyarsa ga Hakimin Nasarawa, Hakimin Gunduma, sauran Dagatai da Masu Unguwanni bisa goyon baya da haɗin kai da suka ba shi.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai ’yan siyasa, ’yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati da malaman addini. Daga cikin fitattun mutanen da suka halarci taron akwai Sulaiman Gama, sanannen ɗan jarida kuma ɗan siyasa, da Anas Yarima Ƙaura Goje, da sauran al’umma da dama.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength