Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Alhaji Abdullahi Sulaiman, wanda aka fi sani da Ɗanjummai, ɗaya daga cikin aminan sabon Dagacin Ƙaura Goje, Alhaji Ali Ado, ya bayyana cewa naɗin da aka yi masa ba komai ba ne face godiya ga Allah, domin abu ne mai ɗauke da tarihi da ya samo asali tun daga iyaye da kakanni.
Ya ce daga cikin waɗanda suka ba su gagarumar gudunmawa a wannan tafiya akwai Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Hon. Yusuf Imam Ogan Ɓoye, wanda ya ce ƙani ne kuma ɗan’uwa, inda ya tsaya tsayin daka wajen ganin an tabbatar da wannan al’amari.
Danjummai ya kuma gode wa tsohon Shugaban Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Hon. Aranfosu, wanda ya ce shi ne ya ɓuɓɓugo da batun tun da farko, yana mai cewa shi ne ainihin jigon wannan al’amari.
Ya ƙara da cewa a lokacin da Ogan Ɓoye ya samu damar jagorantar ƙaramar hukumar, Allah Ya ba shi ikon tabbatar da abin da aka fara.
Alhaji Abdullahi Sulaiman ya ce saboda haka ne a yau suke cikin farin ciki, kasancewar Ƙaura Goje da Gama abu ɗaya ne kuma suna tare.
Ya bayyana sabon Dagacin Ƙaura Goje, Alhaji Ali Ado, a matsayin mutum mai mu’amala, kula da jama’a da kuma riƙe zumunci da abokantaka.
Ya ce abokinsa ne tun suna ƙanana, kuma har zuwa yanzu suna tare ba tare da wani abu ya raba su ba, har suka kai ga wannan matsayi.
Alhaji Abdullahi Sulaiman ya ce sarautar ba sabuwa ba ce ga Ali Ado, domin mahaifinsa, Alhaji Ado Mai Unguwa, tun yana raye, Ali ya kasance yana taimaka masa wajen gudanar da ayyukan da suka shafi al’umma. Ya ce hakan ya sa mulki ya zama kamar gado a gare shi.
Ɗanjummai ya ce duk da cewa suna murnar naɗin Ali Ado a matsayin Dagacin Ƙaura Goje, bai kamata a ɗauki lamarin a matsayin abin murna kawai ba, domin matsayi ne mai ɗauke da babban nauyi, kuma Allah zai tambayi duk wanda Ya ba wa mulki a kan yadda ya gudanar da shi.
Ya ce abin da sabon dagacin yake buƙata shi ne ya yi adalci, ya riƙe gaskiya ga mai ƙarfi da mara ƙarfi, tare da bai wa kowa haƙƙinsa da kuma faɗin gaskiya idan wani al’amari ya zo gabansa.
Ya kuma yi kira ga al’ummar yankin da su yi biyayya ga wanda Allah ya ba wa mulki, su bi shi gwargwadon yadda Shari’a ta tanada, yayin da shi kuma yake ba su haƙƙoƙinsu.






