A hukumance an ƙaddamar da rabon magunguna kyauta da kayayyakin kula mata masu juna biyu da jarirai (Mama Kits) kyauta ga mazauna Kaduna ta Kudu.
Wannan shiri dai cika alƙawuran da Hon. Rayyan Hussein ya ɗauka a yaƙin neman zaɓe na ƙarfafa fannin kiwon lafiya a ƙaramar hukumar Kaduna ta Kudu, bisa manufa ta Gwamna Sanata Uba Sani.

Ƙaddamar da shirin ya samu halartar ’yan majalisa, shugabannin gargajiya da na addini, da masu riƙe da muƙaman ƙananan hukumomi, masu ruwa da tsaki a fannin kiwon lafiya, da sauran jama’a.
A lokacin da yake gabatar da jawabi, Hon Rayyan Hussein ya sake tabbatar da sadaukarwarsu ta sanya inganta ayyukan kiwon lafiya a sahun farko da kuma ɗaukar ƙwararan matakai don rage yawan mace-macen mata masu juna biyu.

Wasu daga cikin baƙin da aka gayyata, a nasu jawabin, sun yaba da gagarumin ci gaban da aka samu a fannin kiwon lafiya a ƙarƙashin gwamnatin Sanata Uba Sani, tare da ƙarfafa gwiwar ci gaba da gudanar da irin wannan aikin na tallafa wa jama’a.

A wani labarin kuma, jama’ar Kaduna ta Kadu sun bayyana godiyarsu matuƙa kan amincewar da muhimman ayyuka uku masu mahimmanci waɗanda za su inganta haɗin kai, sufuri, da ayyukan tattalin arziki a ƙaramar hukumar.
Ayyukan sun haɗa da kammala hanyar da aka yi watsi da ita daga Old Kachia Road (Zenith Bank Roundabout) zuwa Flour Mills a Bypass, wadda ta haɗa ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun.
Sai kuma kammala Titin Dual Carriage Road, wanda aka yi watsi da shi daga PAN Drive ta Garejin Talabijin zuwa Sabon Tasha, wanda kuma ya haɗa ƙananan hukumomin Kaduna ta Kudu da Chikun.
Bugu da ƙari, akwai sake gina hanyar Zango zuwa Asibitin Yara da titin Musawa a Tudun Wada, Kaduna ta Kudu.







