Bukin Kirsimeti da Sabuwar Shekara: Sarkin Margi na Kano Ya Yi Kiran A Yi Addu’a Don Zaman Lafiya

Daga Ibrahim Muhammad Kano

An yaba da irin ƙoƙarin da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Masarautar Kano ƙarƙashin jagorancin Muhammadu Sanusi II ke yi wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma.

Sarkin ƙabilar Marghi mazauna Jihar Kano, Elder Wadzani Adamu, ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ’yan jarida yayin da ake shirin shiga bukin Kirsimeti da kuma sabuwar shekarar 2026.

Ya jaddada cewa gudummawar da Gwamnatin jihar Kano da Masarautar Kano ke bayarwa wajen samar da zaman lafiya ita ce ginshiƙin cigaban zamantakewa da tattalin arzikin al’umma.

Ya bayyana cewa al’ummar Marghi mazauna Jihar Kano masu son zaman lafiya ne, kuma suna da kyakkyawar alaƙa da Hausawa.

A cewarsa, hakan ya sa suke ci gaba da yin addu’ar Allah Ya ƙara haɗa kan jama’a, Ya kawar da duk wani abu da zai iya janyo rashin zaman lafiya a tsakanin al’umma.

Elder Wadzani Adamu ya ƙara da cewa, sun ji daɗin yadda Masarautar Kano ta girmama ƙabilarsu ta Marghi ta hanyar samar musu da masarauta.

Ya ce burinsu shi ne a ci gaba da tabbatar da zaman lafiya, domin shi ne ke bunƙasa cigaban tattalin arziƙi da walwalar jama’a.

Dangane da gabatowar bukukuwan Kirsimeti da sabuwar shekara, Sarkin ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da ma ƙasa baki ɗaya, Kirista da Musulmi, da su dage da addu’a, tare da mai da komai ga Allah.

Ya ce duk abin da aka saka Allah a cikinsa yana zuwa da sauƙi, kuma yin roƙo gare shi ne mafita ga kowace irin ƙalubale.

Ya kuma yi godiya ga Allah da Ya kai su wannan lokaci na Kirsimeti, tare da jan hankalin mabiya addinin Kirista da su gudanar da bukukuwan cikin lumana, su guji almubazzaranci da aikata abin da bai dace ba, tare da bin umarnin Ubangiji domin hakan ne zai taimaka wajen gina al’umma nagari.

A ƙarshe, Elder Wadzani Adamu ya yi addu’ar cewa kamar yadda suka ga farkon shekarar 2025, haka Allah Ya kai su shekarar 2026 cikin albarka, zaman lafiya da cigaba.

Ya roƙi Allah Ya yaye dukkan matsalolin da aka fuskanta a 2025, Ya kuma kawo wa jihar Kano da ƙasa baki ɗaya lafiya, ci gaba da duk abin da ake buƙata na rayuwa.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo