Daga Ibrahim Muhammad
Gamayyar Ƙungiyar Matasan Arewa na APC da aka fi sani da Merger Group APC ƙarƙashin jagorancin Hon. Musa Mujahid Zaitawa ta nuna rashin amincewarta da wasu da ke ƙoƙarin ɓata sunan shugaban Hukumar jin daɗin Alhazzai na ƙasa Farfesa Abdallah Saleh Pakistan ta neman jingina shi da zargin cin hanci da rashawa.
A yayin wani taron manema labarai, ƙungiyar ta koka sosai game da wani bincike da ke gabanta da wasu ɓata-gari daga cikin ma’aikatan Hukumar Aiki Hajji ta ƙasa NAHCON da ke da alaƙa a cikin badaƙalar kuɗaɗen da ake zargi da tuhumar tsohon Shugaban Hukumar ya yi, amma suke son karkatar da hankali da neman ɗora laifin kan shugabancin
Hukumar na yanzu.
Ƙungiyar Matasan da ke ƙarƙashin jagorancin Hon. Musa Mujahid Zaitawa ta nuna goyon bayanta ga Shugaban Hukumar NAHCON, Farfesa Abdallah Saleh Usman Pakistan sakamakon gamsuwa da irin ƙwazon da ya yi na gudanar da aikin Hajjin bana bisa gaskiya da amana cikin nasara da wannan yake nuna ƙoƙarin barin kyakkyawan tarihin da a Hukumar ba a samu a shugabanninta na baya ba.
Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta APC sun ƙara jaddada goyon bayansu game da irin ƙoƙarin da shugaban Hukumar jin daɗin Alhazzai na ƙasa, Farfesa Abdallah Saleh Usman yake na ganin ana gudanar da aikin Hajji cikin tsari mai kyau da nasara da tabbatar tafiyar da Hukumar a tsari na gaskiya da babu cin hanci da rashawa a ciki.







