GWAMNA DAUDA LAWAL YA AMINCE ƘARIN ALBASHIN WATA ƊAYA GA MA’AIKATAN ZAMFARA

Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da biyan ƙarin albashin wata ɗaya ga ma’aikatan gwamnatin Jihar.Shugaban ma’aikata na jihar Zamfara ne ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da aka bayar a ranar 28 ga watan Disamba 2024.Albashin wata na 13 shi ne irinsa na biyu a tarihin jihar Zamfara, inda gwamnatin Lawal ta biya na farko a watan Disambar bara.Ma’aikatan gwamnatin jihar Zamfara da suka haɗa da waɗanda suka yi ritaya, za su samu alawus na kashi talatin bisa ɗari na albashin su a matsayin garaɓasar ƙarin albashin guda, wanda ya zama albashin 13.Wannan shiri ya nuna irin yadda aka aminta da ƙwazon ma’aikatan Zamfara ta hanyar ba su tallafin kuɗi a lokacin hutun ƙarshen shekara.Biyan albashin na watan 13 na ɗaya daga cikin dabaru da dama na ƙarfafa wa ma’aikata gwiwa da bunƙasar tattalin arziki a Jihar Zamfara.Domin cika alƙawuran da ta ɗauka, gwamnati ta cika sama da Naira biliyan 10 na kuɗaɗen alawus-alawus da ake binta a cikin shekaru 11 da suka gabata, ta kuma amince da mafi ƙarancin albashi na Naira 70,000, tare da tabbatar da biyan albashin ma’aikata kan lokaci.

Related Posts

Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You Missed

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo