Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Jam’iyyar NDC reshen Jihar Kano ta yi kira ga Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Sani Hanga da tsohon Gwamnan Kano tsohon sanatan Kano ta kudu Kabiru Ibrahim Gaya, da su janye daga shirin komawa jam’iyyar APC da ake zargin suna yi.
Shugaban NDC na Kano Hon.Hussaini Isah Mairiga, ya ce jam’iyyar za ta yi babban rashi idan manyan biyu suka fice. Ya bayyana cewa har yanzu ba su samu takardar murabus a hukumance daga gare su ba.
“Mu na kira gare su da su dakatar da wannan shiri. Ku zo mu zauna mu tattauna. Duk matsalar da take akwai hanyar warware ta,” inji Mairiga.
Ya kara da cewa duk da ganawar da Hanga da Gaya suka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa Barau Jibrin a Abuja, har yanzu NDC na daukarsu a matsayin mambobinta.
Jam’iyyar ta ce za ta ci gaba da.barin kofar ta a bude ga dukkan ‘ya’yanta domin karfafa jam’iyyar a Kano.
Akan.wannnan dambarwa ta zaton.ficewar Sanata Hanga daga NDC ko a kwanakin.baya ya yi.taro.da.magoya.bayansa domin suje su yanke hukunci abinda yakamata suyi zama a NDC ko.sauya jam’iyya da a halin ake ciki mukarraban.sanatan.da cewa ADC da APC na zawarcinsu.






