Hon. Ibrahim S.B. Maisallah Ya Yaba da Taron Karramawa da Dawakin Tofa Academic Forum Ta Shirya

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Dan takarar Majalisar Jiha na Dawakin Tofa a jam’iyyar NDC, Hon. Ibrahim S.B. Maisallah, ya bayyana taron da kungiyar Dawakin Tofa Academic Forum ta shirya na karrama ‘yan Dawakin Tofa da suka bayar da gagarumar gudummawa ga kasa baki daya, ba Dawakin Tofa kadai ba, a matsayin abin koyi da ke nuna irin gudummawar da magabatan yankin suka bayar har suka bar duniya.

Da yake zantawa da ‘yan jarida a yayin taron, Hon. Ibrahim S.B. Maisallah ya ce

“Wannan irin taro ba wai don tunawa da su kadai ba ne, ana nufin mu tuna da su tare da dora kan abubuwan alheri da suka yi. Yadda aka taru a wajen taron, tun daga matasa, malamai, ‘yan siyasa, ‘yan kasuwa da farfesoshi, ya nuna cewa Dawakin Tofa gari ne mai girma da ma Najeriya gaba daya za ta iya alfahari da da ita”

Hon. Maisallah ya yi kira ga al’ummar Dawakin Tofa da su ci gaba da hada kai, duk da banbancin ra’ayin siyasa da sana’o’i.

“Ko da yake kowa na da nasa tsarin siyasa, wasu ‘yan kasuwa ne, wasu malamai ne, wasu manoma ne, amma yana da kyau mu hada kai, mu ajiye siyasa a gefe, mu hada karfi da karfe domin taimakon al’umma da kuma dorawa kan irin kyawawan ayyuka da magabata suka yi, wanda har ya kai ga shirya irin wannan taro na karrama su, wanda ya zama abin alfahari ga iyalansu da al’ummar Dawakin Tofa baki daya,” in ji shi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo