Daga Ibrahim Muhammad Kano.
Hukumar tsaron al’umma “Civil Defence” ta jihar Kano ta sauke shugabar ofishinta na ƙaramar hukumar Fagge, SC Amina Musa Kolawole, tare da maye gurbinta da CSC Bashir Isa Abubakar.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Hukumar ta jihar Kano, SC Ibrahim Idris Abdullahi, ya fitar aka raba wa manema labarai
Sanarwar ta bayyana cewa matakin ya biyo bayan wani lamari da ya haifar da mutuwar wani matashi mai suna Halifa Abdullahi Fagge.
Tun da farko, Babban Kwamandan Hukumar ta Civil Defence na Jihar Kano, Mohammad Hassan Agalama, ya janye dukkan jami’an da ke bakin aiki a lokacin da lamarin ya faru a ofishin Hukumar da ke ƙaramar hukumar Fagge ta miƙa su.
Haka kuma, Hukumar ’yan sandan jihar Kano domin ci gaba da gudanar da bincike.
Hukumar tsaro ta al’umma ta jihar Kano ta bai wa al’ummar jihar tabbacin cigaba da kare haƙƙin jama’a da tabbatar da adalci a kowane lokaci.







