Hukumar Samar Da Magunguna Ta Jihar Kano Ta Fara Bukin Cika Shekara 3 Na Gwamnatin Abba Da Shirye-Shiryen Mako Guda

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar, Pharmacist Ghali Sule, ta fara gudanar da shirye-shiryen bikin cika shekara uku na gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda zai gudana har tsawon mako guda.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na Hukumar, Faruk Isa Musa, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a madadin Darakta Janar.

Ya ce an fara bukin ne a ranar Litinin da saukar Alƙur’ani Mai Girma da addu’o’i na neman zaman lafiya ga Jihar Kano da Nijeriya baki ɗaya, tare da roƙon Allah Ya ƙara wa Gwamna Abba Kabir Yusuf nasara da ba shi ikon kammala wa’adinsa cikin nasara, tare da sake ba shi damar ci gaba da yi wa al’umma hidima.

A cewarsa, a ranar Talata hukumar za ta gudanar da shirye-shiryen wayar da kan jama’a ta kafafen yaɗa labarai, inda za a bayyana ayyukan da ta gudanar da kuma nasarorin da gwamnatin jihar ta samu a ɓangaren lafiya da sauran fannoni.

Ya ƙara da cewa a ranar Laraba za a gudanar da gagarumar lacca kan illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, inda aka gayyaci ƙwararru daga hukumomi daban-daban, ciki har da Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Hukumar NAFDAC, da kuma wani malamin addinin Musulunci da zai yi bayani kan illar shaye-shayen miyagun ƙwayoyi daga mahangar addini.

Faruk Isa Musa ya ce ana sa ran Gwamna Abba Kabir Yusuf zai halarci taron ranar Alhamis domin ƙaddamar da sabon katafaren rumbun adana magunguna da aka gina a jihar.

Ya bayyana cewa kafin gina wannan rumbu, ana kai magungunan da aka kawo Kano zuwa Jihar Sakkwato domin adanawa kafin daga bisani a dawo da su Kano. Sai dai ya ce sabon rumbun zai inganta tsarin adana magunguna da tabbatar da ingancinsu, lamarin da zai ƙara haɓaka ayyukan kiwon lafiya a jihar.

Ya kuma ce tun bayan da Pharmacist Ghali Sule ya zama Darakta Janar na Hukumar, an samu gagarumin ci gaba wajen samar da magunguna a asibitocin gwamnati.

“A baya, idan likita ya rubuta wa mara lafiya magunguna guda 10, sau da yawa uku ne kawai ake samu. Amma a yanzu, samar da magunguna ya kai kaso 97 cikin 100, wanda ke nufin kusan duk magungunan da aka rubuta wa mara lafiya yana samunsu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa hukumar ta biya dukkan basussukan da ta gada daga gwamnatin da ta gabata, tare da tabbatar da samar da ingantattun magunguna.

A cewarsa, hukumar ta kuma samar da ɗakin gwaje-gwaje na zamani domin tantance ingancin kowane magani kafin a raba shi ga asibitocin gwamnati.

Faruk Isa Musa ya ce baya ga ingancin magungunan, ana sayar da su ne a farashi mai sauƙi.

“Idan aka sayi wani magani a kasuwa kan Naira 2,000, akwai yiwuwar a same shi a asibitin gwamnati da rangwamen da ya kai kusan kashi 40 cikin 100,” in ji shi.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum