Daga Ibrahim Muhammad, Kano
Tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, ya halarci wani babban taron manema labarai da uwar jam’iyyar ADC ta shirya a Abuja.
A yayin taron, jam’iyyar ta koka kan matsalolin da ake zargin suna tasowa tsakanin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) da jam’iyyar ADC.
Jam’iyyar ta ce ta samu labarin fitar da sunayen shugabannin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Sanata David Mark, lamarin da Kwankwaso ya ce ba za su amince da shi ba.
Kwankwaso ya jaddada cewa Hukumar Zaɓe ba ta da ikon kakaɓa wa ‘yan Nijeriya wani ɗan takara, yana mai cewa hakan ya saɓa wa ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Ya ce, “Ina bayar da cikakken goyon baya ga matsayar da wannan taro ya cimma, wadda ke nuna cewa dole ne a bar ‘yan Nijeriya su zaɓi shugabanninsu ta hanyar sahihin tsarin jam’iyyu.”
Ya ƙara da cewa, bai kamata a matsa wa jama’a ko a yi amfani da wata hanya ta ƙarfa-ƙarfa wajen ƙaƙaba musu shugabanni ba, musamman idan aka yi la’akari da cewa Nijeriya ƙasa ce mai girma a Afirka, wadda ke gudanar da dimokuraɗiyya.






