
Mai shari’a Yellim Bogoro na babbar kotun tarayya da ke jihar Legas, ya bayar da umarnin sakin wata dalibar Jami’ar Babcock mai suna Oluwateniola Omidiji da EFCC ta tsare a kan bashin Naira miliyan 100 da mahaifiyarta Misis Omoniyi Omidiji ke bin ta.
Alkalin kotun ya bayar da wannan umarni ne a ranar Juma’a, biyo bayan bukatar da lauyanta, Mista Emeka Chijioke (SAN) ya gabatar na neman a tabbatar mata da hakkinta.
Omidiji mai shekaru 19 ta shafe kwanaki 11 a tsare a hannun EFCC.
Mai shari’a Bogoro ya yanke hukuncin: “Na yi la’akari da bukatar da aka gabatar a baya, da sauran dokoki da aka gabatar da kuma takardar shaidar da ke goyon bayan haka, don haka na yi sassaucin da ake nema,” ya tabbatar.
Jami’an EFCC sun kama Omidiji wata daliba mai mataki 300 na Jami’ar Babcock a harabar makarantar a ranar 26 ga Afrilu, 2024, a lokacin da take rubuta jarabawa.
Daga baya an tsare ta a cibiyar hukumar da ke Ikoyi, Legas, inda aka tsare ta har sai da aka bayar da umarnin Mai shari’a Bogoro a ranar Juma’a, 3 ga Mayu.
A cikin karar da ta shigar mai lamba FHC/L/CS/759/224, Omidiji ta yi zargin cewa jami’an EFCC sun yi garkuwa da ita kan wani bashi da mahaifiyarta ke bin ta.
Nwoko, wacce aka ce ta saka zunzurutun kudi har Naira miliyan 100 a cikin kasuwancin Misis Omidiji a wani lokaci a shekarar 2020, da nufin samun riba tun lokacin da mahaifiyarta, abokin hadin gwiwarsa ta fita Najeriya.
A binciken da EFCC ta gudanar, ta gano cewa an bayyana sunayen mutane hudu a matsayin daraktoci a wani kamfani mai suna Elisto Global Services Limited, wanda Omidiji ta yi amfani da shi wajen karbar kudi daga hannun Nwoko.
EFCC, a lokacin da ta ke kare kanta a gaban kotu, ta ce, tun da aka nada ta a matsayin darakta na kamfanin, Omidiji mai shekaru 19 ya kamata ta amsa laifin da mahaifiyarta ta yi zargin cewa ta aikata a cikin kasuwancin hadin gwiwa da Nwoko.
Sai dai a takardar neman aiwatar da muhimman hakkokinta da lauyanta ya shigar, Omidiji ta bayyana cewa ita ‘yar shekara 16 ce karama a lokacin da mahaifiyarta ta kulla alaka da Mista Nwoko, kuma ba ta san komai ba.
Ta ce ba daidai ba ne hukumar EFCC ta yi garkuwa da ita kan laifin da ake zargin mahaifiyarta ta aikata.
Ta kuma kara da cewa cinikin ya shafi jama’a ne, don haka ta roki kotu da ta umurci EFCC da ta fitar da ita daga cikin lamarin.
Ta kuma roki kotu da ta umurci EFCC ta biya ta Naira miliyan 10 a matsayin diyyar tauye hakkinta na dan Adam, ‘yancin kai da walwala.
Mai shari’a Bogoro, bayan umarnin sakin dalibar, tare da dage ci gaba da sauraron karar har sai ranar 21 ga watan Mayu.







