Kungiyar Jami’ar Siyasa Gangariya Ta Yi Kira Ga Al’ummar Kano Su Yi Rijistar Katin Zaɓe

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Shugaban ƙungiyar Jami’ar Siyasa Gangariya ta Ƙasa, kuma jigo a jam’iyyar APC, Hon. Ado Tati Dala, ya yi kira ga al’ummar jihar Kano da ma na Arewacin ƙasar nan da kada su yi sakaci wajen fitowa domin yin rijistar katin zaɓe, ganin cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta sake fara gudanar da aikin rijistar a faɗin ƙasar nan.

Da yake jawabi ga manema labarai, Hon. Ado Tati Dala ya bayyana cewa katin zaɓe na da matuƙar muhimmanci, domin shi ne ke bai wa ɗan ƙasa damar zaɓar duk wanda yake ganin ya dace ya wakilce shi a kowane mataki na zaɓe.

Ya ce, “Duk wata soyayya ko goyon baya da ɗan ƙasa yake yi wa ɗan takara, ba za ta tabbata ba sai da katin zaɓe. Shi ne ke ba ka damar nuna ra’ayinka a fili.”

Hon. Ado Tati Dala ya ƙara da cewa katin zaɓe na bai wa al’umma damar nuna gamsuwa ko rashin gamsuwa da shugabannin da suka zaɓa a baya, ta hanyar sake zaɓar wanda suka yarda da shi ko kuma sauya shi da wani.

Ya yi nuni da cewa jihar Kano cibiya ce ta siyasa a Nijeriya, kuma ita ce jiha mafi yawan al’umma, don haka ya zama wajibi al’ummarta su fito su yi rijistar katin zaɓe, ta yadda Kano za ta kasance jiha mafi yawan masu katin zaɓe a faɗin ƙasar nan.

Ya ce a matsayinsu na ’yan siyasa kuma ƙungiya mai rajin wayar da kai, Jami’ar Siyasa Gangariya za ta ci gaba da wayar da kan al’umma tare da ba su goyon baya domin tabbatar da cewa sun yi rijista tare da karɓar katin zaɓensu.

Hon. Ado Tati Dala ya kuma yaba da ƙoƙarin Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf, bisa matakan da yake ɗauka na wayar da kan al’ummar jihar kan muhimmancin yin rijistar katin zaɓe da kuma karɓarsa.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength