Ramadan: Hon. Aminu Muktar Ɗan’amu Ya Raba Tallafin Kayan Abinci Ga Marayu 501 Da ’Yan APC A Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Babban Daraktan Kadarorin Kula da Gwamnatin Tarayya, Hon. Aminu Muktar Ɗan’amu, ya raba tallafin kayan abinci ga gidajen marayu 501 da kuma ’yan jam’iyyar APC a ƙaramar hukumar Birnin Kano, domin tallafa musu yayin da ake tunkarar watan Azumin Ramadan.

Tsohon Gwamnan jihar Kano kuma tsohon Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya yaba da wannan shiri, yana mai cewa lokaci ne da ya dace domin sauƙaƙa wa al’umma shirye-shiryen azumi, musamman ganin muhimmancin tanadin abinci ga iyalai.

Ya bayyana cewa waɗanda za su karɓi tallafin wakilai ne na sauran jama’ar da za su ci gajiyar abincin, tare da roƙon su da su riƙa yi wa Aminu Ɗan’amu addu’a.

Haka kuma ya gode wa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa turo Kwamishinan Yaɗa Labarai domin halartar taron.

Ganduje ya ƙara da cewa Aminu Ɗan’amu tsohon Kwamishinansa ne na Kuɗi, mutum mai natsuwa, ilimi da hangen nesa, wanda tun bayan samun muƙami a Gwamnatin Tarayya yake ƙoƙarin taimakawa al’umma ta hanyoyi daban-daban.

Ya kuma nuna cewa Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya ba shi wannan muƙami ne domin ƙara nuna muhimmancin jihar Kano a matakin ƙasa.

A nasa jawabin, Shugaban APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya gode wa Aminu Ɗan’amu, yana cewa irin wannan aiki ya dace da aƙidar jam’iyya, tare da jaddada cewa shugabanni da masu neman muƙami su riƙa tallafawa jama’a musamman marayu.

Ya ce bayar da tallafin abinci babban aiki ne mai lada, kuma jam’iyyar za ta ƙara ƙaimi wajen taimakon al’umma a lokacin azumi.

Shi ma Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar Kano, Ibrahim Waiya, ya bayyana cewa rabon tallafin ya dace da manufofin gwamnatin jihar na taimakon mabuƙata, yana mai tunatar da shirin ciyar da dubban mutane da ake yi a watan Azumi.

Tun da farko a jawabinsa, Aminu Ɗan’amu, Babban Daraktan Hukumar Kula da Kadarorin Gwamnatin Tarayya ya ce ya shirya rabon tallafin ne domin rage raɗaɗin rayuwa ga marayu da mabukata, yana mai cewa ya saba yin irin wannan taimako tun a baya.

Ya bayyana cewa gidajen marayu 501 ne suka amfana, yana mai cewa shi ma maraya ne, kuma hakan na sa ya fi fahimtar halin da suke ciki.

Ya kuma yi kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su ma su riƙa taimaka wa maƙwabta da masu buƙata ko da da kaɗan ne.

Taron rabon tallafin ya samu halartar jiga-jigan jam’iyyar APC, masu unguwanni, wakilai da ’yan siyasa maza da mata daga sassa daban-daban na ƙaramar hukumar.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength