Kungiyar Kasuwar Waya Ta Bata Global Kano Ta Sa Masu Abinci Su Sassauta Farashi

Daga Ibrahim Muhammad

Sakamakon sauƙin farashin kayan abinci da aka samu, ƙungiyar masu harkar sayar da waya ta kasuwar Bata Kano da aka fi sani da “Bata Global GSM Market” ƙarƙashin jagorancin shugabanta na riƙo Hon. Mahrazu Usman Lawan sun ɗauki matakin haɗa kai da masu sayar da abinci da ke kasuwar don sauƙaƙawa al’umma.

Da yake zantawa da ‘yan jarida, shugaban ƙungiyar Hon. Mahrazu Usman Lawan ya ce, “Abin da ya jawo hankalinsu na ɗaukar matakin shi ne su da suke kawo waya a kasuwar yanzu canji ya sauka, kuma dalilin wannan an sami sauƙin kayan abinci, amma sai suka ga yadda za ka je ka miƙa kuɗi a ba ka abinci dafaffe a baya ya ki sauyawa a wajen masu sayarwa, kuma ya kamata a ce in abinci yau ya yi sauki a gane sauƙin a zahiri, saboda idan ya yi tsada su ƙara mana kuɗi mu yarda.”

Ya ƙara da cewa amma yanzu ana cikin wani hali sun ƙi sauke farashin zuba abincin, shi ne dalilin da ya sa ƙungiyar ta ɗauki mataki a kasuwar, da bai wuce ƙa’ida ba, suka zauna da masu abincin suka shaida musu su rage farashi in kuma ba za su yi ba, su nemi kamfanoni da suka kai 50 da suka ce za su kawo abinci cikin sauƙi.

Ya ce abin godiya ga Allah shi ne masu abinci a kasuwar sun karɓi gyara, sun amince da rage kuɗin abincin.

“Da sun yarda ne su ƙara yawan abincin, amma ƙungiyar ta ce a’a a zahiri kuɗi suke ƙarawa in ya ƙaru, abin da suke so su rage kuɗin a zahiri yanzu an sami sauƙi, hatta masu awara uku 100 suka mayar, masu abinci suna zuba har na 200 da na 300 har ƙasa da haka, kuma dama abin da muke so ke nan a sami sassauci,” in ji shi.

Ya ce yanzu haka kasuwar waya ta Bata suna da masu sana’ar sayar da abinci da yawansu ya kai sama da 40, amma saboda sun yi ƙorafin cewa abin zuba abinci ya yi tsada, ta ɓangaren ƙungiya sun ba su gudunmuwa na abin zuba abinci sannan ba sa biyan kuɗin shara da na gadi saboda sauƙaƙa musu, ganin yawanci masu karamin ƙarfi ne, wannan duk sun ɗauke musu, kuma mafi yawansu ƙungiyar ce ta ba su wajen zama da suke sana’a.

Hon. Mahrazu Usman Lawan ya ce, kasuwar su ta waya ta Bata tana samun cigaba sosai da bunƙasa kullum. A matsayinsu na shugabanni sun ɗora kasuwar a kan turba mai kyau ƙari a kan yadda shugabanin baya suka yi, shi ya sa ta sami nasarar zuwa mataki da take a yanzu.

Ya ce a tsarin su na jagorancin ƙungiyar kasuwar a halin yanzu ba su da wata rarraba a tsakaninsu kansu a hade yake, suna aiki tare da kowane ɓangare domin samar da cigaba, babu wata hayaniya a kasuwar kowa na kasuwancinsa daidai gwargwado.

Hon. Maharazu ya ce a ɓangaren inganta tsaro ba su da matsala suna da kyakkyawar alaƙa da jami’an tsaro har ta kai ma ba sa shigowa kasuwar, idan ana zargin wani ɗan kasuwar da laifi ƙungiyar kasuwar da kanta take miƙa shi ga Hukuma, idan kuma sun tabbatar ba shi da laifi za su je su karɓo shi.

Ya yi nuni da cewa akwai dubun-dubatar matasa da suke sana’ar waya a jihar Kano a ɓangarori daban-daban, wasu na gyaranta suke, wasu na sayar da kayan gyaran iri daban-daban, wani batir, wani na sayar da sabbi, kuma zai wahala a je wani gida a Kano a rasa matashi da yake harkar waya idan ba ya yi a kasuwa yana yi a unguwa.

Shugaban rikon na ƙungiyar kasuwar waya ta Bata Global, Hon. Mahrazu Usman Lawan ya yi kira ga ‘yan kasuwar a kan su cigaba da ba su haɗin kai da goyon baya don cigaba da tsare musu harkokinsu, kuma su riƙe gaskiya da amana a gudanar da harkokin kasuwancinsu na waya.

  • Related Posts

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Daga Al-Amin Ciroma Mai ba Hon. Ibrahim Kabir Masari shawara kan harkokin matasa da da koyarda sana’o’i, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, ya bayyana Masari a matsayin ɗaya daga cikin ginshiƙan…

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    By Al-Amin Ciroma An Adviser on Youth and Skills Acquisition to Hon. Ibrahim Kabir Masari, Alhaji Yahaya Bello Potiskum, has described Masari as a key pillar of President Bola Ahmed…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum