An Yi Kira Ga Al’ummar Ungogo Da Minjibir Su Sake Zaɓar Hon. Sani Wakili

Daga Ibrahim Muhammad, Kano.

Wani jigo a tafiyar siyasar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar ƙananan hukumomin Ungogo da Minjibir, Hon. Sani Wakili Adamu, Ibrahim Usman Mshelia Majidadi, ya yi kira ga al’ummar yankunan da su sake zaɓar ɗan Majalisar a karo na biyu a ƙarƙashin jam’iyyar NDC domin ba shi damar ci gaba da ayyukan da yake gudanarwa a yankin.

Ibrahim Usman Mshelia Majidadi ya bayyana cewa tun bayan zuwansa Majalisar Tarayya, Hon. Sani Wakili Adamu yake ƙoƙarin sauke nauyin da ke kansa ta fannoni daban-daban, musamman waɗanda suka shafi bunƙasa rayuwar al’umma da samar da hanyoyin ci gaba a ƙananan hukumomin Ungogo da Minjibir.

Ya ce a matsayinsu na magoya bayansa da ’yan siyasa, sun yi aiki tuƙuru wajen neman masa zaɓe a ƙarƙashin tsohuwar jam’iyyarsu ta NNPP, inda suka shiga lungu da saƙo domin wayar da kan al’umma, musamman mazauna Ungogo, har aka samu nasarar zaɓensa a shekarar 2023.

Mshelia Majidadi ya ƙara da cewa a yanzu ma suna ci gaba da ƙoƙarin haɗa kan al’umma tare da wayar musu da kai kan abin da ya kira muhimmancin sake zaɓar Hon. Sani Wakili a karo na biyu, bisa amincewarsu da shi da kuma yadda suke kallon amana da biyayyarsa ga tafiyar Kwankwasiyya.

“Ko gezau bai yi ba wajen bin tsarin siyasar Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso. Hon. Sani Wakili ya ƙi amincewa a sauya masa akidar siyasa, saboda shi ɗan amana ne da ya san halacci,” in ji Mshelia.

Ya bayyana cewa al’ummar Ungogo da Minjibir sun san irin taimako da tallafin da yake bayarwa ga matasa domin ƙarfafa musu gwiwa su dogara da kansu. Ya kuma yi iƙirarin cewa ana tallafa wa wasu ’yan siyasa da babura, motoci da sauran kayayyaki domin taimaka musu wajen gudanar da harkokinsu da inganta rayuwarsu.

Haka kuma, Ibrahim Usman Mshelia Majidadi ya ce a ƙoƙarinsu na ƙarfafa rajistar masu zaɓe a yankunan, yana bayar da gudunmawar kuɗin mota daga aljihunsa ga wasu iyaye mata da matasa waɗanda ba su da kuɗin sufuri domin su je su yi rajistar zaɓe.

A ƙarshe, ya yi kira ga al’ummar ƙananan hukumomin Ungogo da Minjibir da su yi amfani da damar zaɓe mai zuwa wajen zaɓen ’yan takarar da suke ganin za su wakilci muradunsu, tare da ƙarfafa musu gwiwa su yi la’akari da Hon. Sani Wakili da sauran ’yan takarar jam’iyyar NDC.

  • Related Posts

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Hon Alhaji Bashir Abubakar Galadima, hadimin Gwamnan jihar Kano a ma’aikatar kananan hukumomi, ya bayyana jin dadinsa kan yadda aka kammala gyare-gyaren kasafin kudin shekarar 2027…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength

    Yahaya: Masari Remains Key Pillar Of Tinubu’s Political Strength