Daga Ibrahim Muhammad Kano
Hon. Mustapha Isah Mai Wake ya bayyana cewa al’ummar Ƙaramar Hukumar Fagge da ke jihar Kano za su bai wa tafiyar Kwankwasiyya cikakken goyon baya a cikin jam’iyyar ADC domin kawar da zalunci a ƙasar nan.
Ya bayyana haka ne yayin da yake tsokaci kan taron komawar jagoran Kwankwasiyya, Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso, zuwa jam’iyyar ADC, inda ya ce taron ya zama manuniya cewa al’ummar jihar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya sun karɓi jam’iyyar, kuma suna buƙatar sauyi bisa halin matsin rayuwa da ake ciki.
Mai Wake ya ce sun ji daɗin yadda manyan ‘yan siyasa suka haɗa kai domin dunƙulewa wuri guda da nufin kawar da jam’iyya mai mulki, yana mai cewa suna da ƙwarin gwiwar samun nasara.
Ya lissafa wasu daga cikin manyan ‘yan siyasar da suka haɗu a jam’iyyar ADC da suka haɗa da Kwankwaso, Peter Obi, Atiku Abubakar, David Mark, Rauf Aregbesola, Aminu Waziri Tambuwal, Rotimi Amaechi da Nasir El-Rufa’i, yana mai cewa haɗuwar su na buƙatar goyon bayan al’umma domin cimma buri.
A cewarsa, Ɗan Majalisarsu na Fagge na Jiha da na Tarayya da shugaban Ƙaramar Hukumarsu na yanzu da Gwamna Kano Abba Kabir, falle ɗaya za su yi, ba za su sake zaɓen su ba.
Ya ƙara da cewa Fagge na daga cikin wuraren da aka kafa jam’iyyar NEPU, don haka al’ummarta sun san yadda ake gwagwarmayar neman haƙƙi da kuma kare talaka daga zalunci.
“A nan ana fahimtar bambanci tsakanin gaskiya da ƙarya, da kuma zalunci da adalci, shi ya sa muke sahun gaba wajen yaƙar duk wani tsari da zai cutar da talaka,” in ji shi.
Mai Wake ya ce idan aka yi la’akari da halin da ƙasar nan ke ciki na tsadar man fetur, hauhawar farashin kayan abinci, ƙuncin rayuwa da matsalar tsaro, ya zama wajibi a samu sauyi.
“Saboda haka mu a Fagge muna sahun gaba wajen ganin an kawo karshen mulkin jam’iyyar APC domin ceto kasar nan,” in ji Mai Wake.






