Muna Goyon Bayan Takarar Sanatan Sakkwato Ta Gabas Da APC Ta Tsayar Da Ajiyan Isa -Talban Isa

Daga Ibrahim Muhammad

An bayyana tsayar da Alhaji Umar Ajiyan Isa a matsayin ɗan takarar Sanatan Sakkwato ta Gabas a ƙarƙashin jam’iyyar APC a matsayin mataki da aka ɗauka bisa cancanta, la’akari da irin gudunmawar da yake bayarwa wajen ci gaban al’umma.

Alhaji Shitu Adamu Bargaja, wanda aka fi sani da Talban Isa, ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai.

Ya ce al’ummar yankin sun shirya tsaf domin bai wa takarar Ajiyan Isa cikakken goyon baya tare da tallata shi a faɗin yankunan Sakkwato ta Gabas, saboda yadda jama’a da dama suka san shi da ayyukan alheri.

Ya ƙara da cewa a duk muƙaman da Alhaji Umar Ajiyan Isa ya riƙa a baya, ya nuna jajircewa wajen taimakon jama’a da kyautata rayuwarsu.

A cewarsa, har yanzu yana ci gaba da kula da bukatun al’umma, sannan mutum ne mai kishin cigaban jihar Sakkwato.

Talban Isa ya kuma bayyana cewa Ajiyan Isa na taka muhimmiyar rawa wajen inganta tsaro, tallafawa marasa galihu da ‘yan gudun hijira, da kuma taimakawa al’umma wajen biyan wasu daga cikin bukatunsu na yau da kullum.

Ya ce mutum mai irin waɗannan halaye ne ya dace a mara wa baya domin ya wakilci al’umma yadda ya kamata.

Alhaji Shitu Adamu Bargaja ya ƙara da cewa suna shirye su fito da jama’arsu domin gudanar da yaƙin neman zaɓe ga Ajiyan Isa domin tabbatar da nasararsa a zaɓen Sanatan Sakkwato ta Gabas na shekarar 2027.

Haka kuma ya ce za su mara wa Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu Sokoto, da sauran ‘yan takarar jam’iyyar APC baya domin samun nasara a zaɓen 2027 da yardar Allah.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum