Daga Ibrahim Muhammad, Kano.
Mataimakiyar ɗan takarar gwamnan Jihar Kano a ƙarƙashin jam’iyyar NDP mai alamar fitila, Ambasada Hajiya Sameera Bala Usman, ta bayyana cewa gwamnatinsu za ta mayar da hankali wajen samar da sauyi mai ma’ana da inganta rayuwar al’ummar jihar idan suka samu nasara a zaɓen 2027.
Ambasada Sameera ta bayyana hakan ne yayin da take yi wa ’yan jarida bayani kan dalilan da suka sa ta zaɓi shiga jam’iyyar NDP tare da tsayawa takarar mataimakiyar gwamna, inda ta ce kyawawan manufofin jam’iyyar na bunƙasa rayuwar al’umma ne suka jay hankalinta.
Ta ce jam’iyyun siyasar da suka saba kafa gwamnati a baya ba su ba mata kulawar da ta dace, tare da bayyana cewa wasu daga cikinsu na fuskantar ƙalubalen haɗin kai da samar da manufofin da za su kawo ci gaba mai ɗorewa ga al’umma.
“Jam’iyyun da muke da su waɗanda suke kafa gwamnati ba sa ba mata kulawa yadda ya kamata. Kowacce tana da ƙalubalen rashin haɗin kai da kuma tunkarar manufofin da za su kawo ci gaban al’umma. Saboda haka, mun ga cancantar manufofin NDP, tare da fatan ita ce za ta kawo ci gaban da muke fata,” in ji ta.
Ta bayyana cewa suna da kyakkyawan fata na samun nasara a zaɓen 2027, duba da muhimmiyar rawar da mata suke takawa wajen gina al’umma, musamman a harkokin zaɓe, inda ta jaddada cewa ya kamata a ba su dama domin su bayar da gudunmawarsu wajen tafiyar da harkokin gwamnati.
Ambasada Sameera ta ce samun damar zama mataimakiyar ɗan takarar gwamna a jam’iyyar NDP ya samo asali ne daga ƙwarewarta da kuma gwagwarmayar siyasar da ta daɗe tana yi.
Ta bayyana cewa a baya ta taɓa tsayawa takarar sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, kafin sauye-sauyen da suka faru a siyasar jam’iyyar su sa ta sake duba matsayinta, daga bisani ta koma NDP saboda kyawawan manufofinta.
Ta ce daga cikin manyan abubuwan da za su ba muhimmanci idan suka samu nasarar kafa gwamnati akwai bunƙasa rayuwar matasa, inganta tsarin karatun almajirai da kuma ƙarfafa ilimin yara da matasa, bisa la’akari da muhimmiyar rawar da ilimi yake takawa wajen ci gaban al’umma.
Haka kuma, ta bayyana cewa za su mayar da hankali wajen taimaka wa matasa su guji shaye-shayen miyagun ƙwayoyi, tare da samar da hanyoyin tarbiyya da shiryar da su zuwa ayyukan da za su amfani rayuwarsu da kuma al’umma baki ɗaya.
Dangane da walwalar mata kuwa, Ambasada Sameera ta ce za su samar da shirye-shiryen koyar da sana’o’in dogaro da kai ga matan aure da zawarawa, domin su samu damar inganta tattalin arzikinsu da kula da kansu da ’ya’yansu cikin sauƙi.
“Gwamnatin NDP idan ta kafa gwamnati, ba za ta tsaya kawai kan gine-ginen gadoji da hanyoyi domin kawata tituna ba, kamar yadda wasu gwamnatoci suke yi. Za mu gudanar da ayyukan da za su kyautata rayuwar al’umma, tare da kula da harkokin tsaro tun daga tushe,” in ji ta.
A ƙarshe, Ambasada Hajiya Sameera Bala Usman ta yi kira ga al’ummar Jihar Kano, musamman matasa da mata, da su ba jam’iyyar NDP cikakken goyon baya da haɗin kai domin samun nasara a babban zaɓen shekarar 2027.






