Daga Ibrahim Muhammad
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya kai ziyara kasuwar wayoyi ta Farm Centre da ke Kano ya jajanta wa ’yan kasuwar game da gobara da aka yi ranar Juma’ar da ta gabata.
A yayin ziyarar da ya kai ranar Lahadi, Sanata Barau Jibrin, wanda kuma shi ne mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, ya bayar da tallafi na kayan da ake saidawa a wurin da aka yi gobara da suka kai kimanin Naira miliyan 200 domin rage raɗaɗin asarar da gobarar ta haifar wa ’yan kasuwar.
A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Ismail Mudashir, ya fitar, Sanata Barau ya bayyana wannan ibtila’i a matsayin jarrabawa daga Allah, tare da jaddada muhimmancin kasuwar wajen samar da aikin yi ga matasan jihar.
Sanata Barau ya kuma bayyana cewa zai bayar da motar ƙirar Hilux guda ɗaya, babura guda biyar (5), da fitilun titi na hasken rana guda dubu daya (1,000) domin tabbatar da tsaron kasuwar.
Haka zalika, zai gina gada ta tsallaka titi domin sauƙaƙa zirga-zirga da tsare lafiyar masu tsallaka titi.
“Da na samu labarin gobarar nan a ranar Juma’a, na ji matuƙar damuwa, kuma nan take na ƙuduri aniyar zuwa domin jajanta muku. Wannan kasuwa tana da matuƙar muhimmanci saboda yadda matasa ke samun halalinsu a cikinta.
“Saboda haka, ofishina zai ba da tallafi na kaya da ya kai Naira miliyan 200 ga waɗanda gobarar ta shafa. Za mu tattauna da shugabanninku domin a tantance nau’in kayan da suka fi dacewa.
“Sannan kuma bisa buƙatar shugaban kasuwar na inganta tsaron kasuwa, na bayar da gudunmawar fitilun titi 1,000, motar Hilux guda ɗaya da babura guda biyar.”
A nasa jawabin, shugaban kasuwar, Jamilu Bala Gama, ya gode wa Sanata Barau bisa wannan ziyara da tallafin da ya bayar.
“Mai girma Sanata, kai ba kawai Sanatan Kano ta Arewa ba ne, kai Sanatan al’umma ne gaba ɗaya. Ka wuce iyaka na wakilci. Allah ya saka maka da alheri,” ya bayyana.







