Shekaru 2 A Mulkin Kano: ‘Mun Gamsu Da Kamun Ludayin Gwamna Abba Kabir Yusuf’

Daga Ibrahim Muhammad

Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Talban Panshekara, Hon. Isyaku Yahaya ya bayyana shekaru biyu da rantsar da zaɓaɓɓen Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin Gwamna da cewa yana tafiyar da Kano bisa adalci da jajicewa wajen yin aiki tuƙuru don kyautatawa cigaba da bunƙasa al’ummar jihar.

Ya bayyana hakan ne da yake zantawa da ‘yan jarida ya ce zuwan gwamnatin nan ta taradda abubuwa a jihar Kano kusan a dagule kama daga kan harkokin ilimi da lafiya da rashin kyautatawa ma’aikata da kuma yadda ake sayar da kadarorin jihar Kano da gwamnatin da ta gabata take suka hatta asibitin kula da ƙananan yara na Asiya Bayero sai da aka sayar da shi da kuma ajujuwa da filayen makarantu.

Hon. Alhaji Isyaku Yahaya ya ce daga rantsar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf zuwan sa ya soma da ƙoƙarin dawowa jihar Kano martabar ta a idanun duniya ya karɓo asibitin yara na Asiya aka gyara shi yanzu yana aiki awa 24 ana kula da yara marasa lafiya kyauta.

Ya ce kowa ya san a tsarin su na tafiyar Kwankwasiyya babban abin da suka fi bai wa muhimmanci shi ne bunƙasa ilimi. Don haka ma ba a jima da rantsar da shi ba aka tura ɗaruruwan ɗalibai ‘ya’yan talakawa da suka cancanta ba tare da la’akari da bambancin siyasa ba manyan makarantu a ƙasashen duniya domin yin karatun digiri da tuni wasu ma har sun kammala.

Ya ƙara da cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ganin harkar ilimi ya inganta a jihar Kano ya sanya dokar ta-ɓaci a kan ilimi ana warewa ilimi kaso mafi yawa a kasafin kuɗi ana aikin gyaran makarantun Firamare da na Sakandire a ƙananan hukumomin da ke ƙwaryar birni da na karkara ana samar musu da kujerun zama da kayan aiki, tare da dawo da makarantun kwana da gwamnatin Ganduje ta rufe su ana kuma biyawa ɗalibai kuɗin jarabawar NECO da na JAMB.

Ya ce an kyautata tsarin biyan albashin ma’aikata a kan lokaci musamman malaman makaranta ana yi musu ƙarin girma na aiki da aka daɗe a baya ba a yi musu ba. Wannan ya sanya farin ciki a zukatan malamai har iyaye suka sami ƙwarin gwiwa na sanya ‘ya’yansu a makarantu saboda ana ba su kayan makaranta kyauta.

Ya ce haka a ɓangaren manyan makarantu ya ragewa ɗalibai da suka shiga manyan makarantun gwamnati kuɗin rijista da kuma dawo da manyan makarantun koyon sana’o’i da aka samar lokacin da jagoransu na Kwankwasiyya Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso yake Gwamnan jihar Kano, amma lokacin gwamnatin Ganduje ya rufe su.

Ambasada Alhaji Isyaku Yahaya ya ce, haka idan aka dubi fannin kula da lafiya an gyara manyan asibitoci don sama musu yanayi mai kyau domin kula da lafiyar al’ummar jihar Kano.

An gyara sashin karɓar marasa lafiya na gaggawa na asibitin ƙwararru na Murtala Muhammad da gyara a sassa da dama na asibitin da yin gyara da samar da sabbin gine-gine a asibitoci da ke faɗin jihar Kano da samar musu da kayan aiki.

Talban Panshekara ya ce, wani abin jin daɗi shi ne gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta samar da kyakkyawan yanayi da mata masu juna biyu za su rika haihuwa kyauta a asibitocin jihar Kano da kuma ɗaukar matakan gaggawa wajen yin riga kafin a kan cutuka masu yaɗuwa domin kare al’ummar Kano.

Ya ce, gwamnatin jihar Kano tana gudanar da ayyukan hanyoyin manyan gadoji na ƙasa da na sama a Ɗan’agundi da Tal’udu da kuma gyara manyan hanyoyi da ƙanana da haskaka titunan jihar Kano da fitilu masu aiki da hasken rana da kuma biyan kuɗaɗen fansho a kai a kai. Sannan ya zo ya biya tsofaffin Kansilolin APC da gwamnatin da wuce ba ta biya su ba, sannan kuma ana tallafa wa mata da matasa da jari a kai a kai a ƙananan hukumomi 44 don su dogara da kansu.

“Gwamna Abba yana gudanar da muhimman ayyuka a fannoni da dama da ba za su lissafu a ƙaramin lokaci ba,” in ji shi.

Ya ce su a matsayinsu na shugabannin a jam’iyyar NNPP na jihar Kano suna mutuƙar alfahari da Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, yana sauke nauyin da al’umma suka zaɓe shi a kai. Cikin shekaru biyu ya mayar da jihar Kano abin kwatance wajen gudanar da ayyuka.da yake. Ya rufe bakin ‘yan hamayya, domin daga cikinsu ma akwai waɗanda suke fitowa suna yabawa ƙwazon Gwamna kan ayyukan da yake.

Ambasada Alhaji Isyaku Yahaya Talban Panshekara ya yaba wa alummar jihar Kano bisa irin goyon baya da suke bai wa jagoransu na Kwankwasiyya Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso da gwamnatinsu ta NNPP, tare da yin kira a gare su su cigaba da taya Gwamna Abba Kabir Yusuf da addu’ar Allah ya cigaba da ba shi ikon gudanar da ayyuka da yake aiwatarwa na bunƙasa cigaban jihar Kano.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum