Shekaru 69: Kwankwaso Shugaba Ne Mai Hangen Nesa Da Jajircewa -Talban Fanshekara Ambasada Isyaka Yahaya

Daga Ibrahim Muhammad

Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Ambasada Isyaka Yahaya Taliban Fanshekara, ya taya tsohon Gwamnan jihar Kano, kuma tsohon ministan tsaro madugun Kwankwasiyya, Sanata Dakta Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso murnar cika shekaru 69 a duniya.

Ya ce Sanata Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso ɗan siyasa ne na gaskiya jagora, kuma shugaba mai hangen nesa, wanda jajircewarsa na tabbatar da adalci, daidaito da kuma ci gaban ƙasa ke ci gaba da ƙarfafa kyakkyawan fata a faɗin Nijeriya.

Ya ce tsohon Gwamnan jihar Kano Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso a tsawon shekaru ya nuna kyakkyawan jagoranci, jajircewa da sadaukarwa ga ci gaban jihar Kano, Arewacin Nijeriya da ƙasa baki ɗaya.

Ya yi nuni da cewa a tasirinsa kan siyasa da mulki na da ban mamaki da kullum yake daɗa karɓuwa saboda irin kyawawan manufofinsa ga al’umma.

Mataimakin shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Ambasada Isyaka Yahaya ya yi addu’ar Allah ya ƙara wa Jagoran Kwankwasiyya Dakta Rabi’u Musa Kwankwaso lafiya, lafiya da hikimar ci gaba da jagoranci da bayar da gudunmawa ga cigaban Nijeriya.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum