Shin Da Gaske Ne Ɗan Majalisar Tarayya Na Ƙaramar Hukumar Birnin Kano Ya Fice Daga NNPP?

Daga Ibrahim Muhammad Kano

Tun a farkon makon nan ne ake yaɗa wani labari a kafafen sada zumunta da ba shi da tabbas na cewa zaɓaɓɓen ɗan Majalisar Tarayya a ƙarƙashin jam’iyyar NNPP mai wakiltar ƙaramar hukumar Birnin Kano, Hon. Injiniya Ɗahiru Ibrahim Ƙoƙi ya fice daga jam’iyyar ya koma APC.

Dama dai tun kafin wannan a baya akwai masu ƙalubalatar ɗan Majalisar da cewa yana shirin barin jam’iyyar sai dai ana ganin masu adawa da shi ne na cikin gida ke yaɗa hakan don rage masa karsashi.

Sai duk bincike da muka yi a tsakanin ‘yan jam’iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Birni da wasu daga magoya bayan ɗan Majalisar sun bayyana cewa ba su da masaniyar cewa ya bar jam’iyyar NNPP.

Sun yi zargin cewa kawai ‘yan adawa ne na cikin gida da suke zargin ɗaya daga cikin masu muƙamai a jam’iyyar da suke hamayya da ɗan Majalisar ke ƙulla wannnan kutungwila don dusashe irin karɓuwa da ya yi. “Suna jin haushin irin ayyuka da yake na cigaban al’umma,’ in ji majiyar tamu.

Domin tabbatar da gaskiyar wannan jita-jita da ake yaɗawa ta fitar ɗan Majalisar Tarayyar na ƙaramar hukumar Birnin Kano daga NNPP mun nemi ji ta bakin Injiniya Sagir Ibrahim Ƙoƙi, amma bai ɗauki waya ba, kuma bai amsa saƙon kar-ta-kwana da muka tura masa ba har zuwa lokacin haɗa wannan labarin.

Ɗaya daga cikin makusantar ɗan Majalisar ta tabbatar mana da cewa ba wannan batu na barin jam’iyyar da ake yaɗawa Sagir Koki ya yi ƙaarya ce tsagwaronta ta maƙiya da mahassada ganin cewa babu yadda za su iya ja da shi duba da irin ɗimbin ayyuka da yake da ko a kwana nan ya ƙaddamar da yi wa masu larurarar idanu kyauta ga ayyuka nuna tituna da tallafawa ilimi da sauran al’umma da yake kuma akwai gagarumin tallafi na da zai yi wa al’ummar yankin mazaɓarsa nan ba da jimawa ba.

  • Related Posts

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Dan majalisar dokokin jihar Kano mai wakiltar karamar hukumar Tudun Wada, kuma Minority Whip na majalisar, Hon. Sule Lawan Shuwaki, ya bayyana jam’iyyar sa ta PDP…

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Daga Ibrahim Muhammad Kano Wani Matashi jigo a jam’iyyar NDC Kwankwasiyya daga karamar hukumar Bebeji, Abba Umar Tiga, ya ce tun da aka koma tsarin Damakwaradiyya yankin Kano ta Kudu…

    Leave a Reply

    Your email address will not be published. Required fields are marked *

    You Missed

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    Abin Da Ya Sa Na Bar Jam’iyyar APC -Hon. Sule Lawan Shuwaki

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    2027: Za Mu Haɗa Kai Mu Zaɓi Ibrahim Alkasim Batayya a NDC -Abba Umar Tiga

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gwamna Abba Ya Gabatar Da Kasafin Kuɗin Naira Tiriliyan 1.107 Na 2027, Ya Ba Ayyukan Cigaba Fifiko

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Gyaran Kasafin Kuɗin 2027: Hadimin Gwamna Bashir Abubakar Galadima Ya Yaba Wa Shugabannin Ƙananan Hukumomi 44 Na Jihar Kano

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Ni Ne Halastaccen Ɗan Takarar NDC A Gwale, Kano -Awilo

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum

    Siyasar Tinubu Ta Ta’allaka Kan Amintattun Abokansa Kamar Masari — Yahaya Potiskum